
Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce hakika marigayi Moshood Abiola ya lashe zaben watan Yuni na 1993 wanda gwamnatin sa ta soke.
Janar Babangida na magana ne a Abuja wajen taron kaddamar da littafin tarihin rayuwar sa ta aiki mai taken “A journey in service” da asusun gina dakin karatu na IBB a Minna.
“Na dau alhakin duk abun da gwamnati na ta gudanar, soke zaben 1993 na daga abubuwan da su ka zama masu tsauri a rayuwa ta” Inji Janar Babangida bayan tabbatar da cewa Abiola ya cika dukkan sharuddan lashe zaben wajen yawan kuri’a da kuma samun adadin yankuna.
Janar Babangida ya yabawa gwamnatin tsohon shugaba Buhari don aiyana Abiola a matsayin tsohon shugaban kasa duk da hakan ya faru bayan rayuwar sa.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ya yi btar littafin mai shafi 420 a gaban mahalarta da su ka hada da shugaba Bola Tinubu da Janar Yakubu Gowon ya kawo bayanan yanda Babangida ya kwance damarar Dimka bayan kisan gilla ga Janar Murtala da kuma yanda juyin mulki ya kawo Buhari kan mulki a 1983 har sake juyin mulki a 1985 da Babangida ya hau da labarin su Janar Mamman Vatsa wanda a ka yankewa hukuncin kisa sanadiyyar shirin juyin mulki. Hakanan ya kawo lakabin Babangida da ya hada da MARADONA don yanda ba a gane matakin da zai dauka sai ya cimma nasara sai EVIL GENIUS da ke nuna hatsabibancin sa a aikin soja.
Janar Muhammad Barau mai ritaya ya ce ya yi aiki da Janar Babangida kuma har yau bai ga wanda ya yi aiyukan raya kasa irin sa ba “b azan iya lissafa ma ka irin aiyukan raya kasa da ya gudanar ba. Har yanzu ba wanda ya yi irin na shi amma ba mai magana ba ne”
Wasu Katsinawa ma da Babangida ya fara kirkiro mu su jiha a 1987 da Akwa Ibom sun nuna ba za su manta da tarihin ba.
Babangida wanda ya ce yanzu ya na shirin cika shekaru 84 a duniya ya yi fatan ko bayan ran sa dakin karatun sa ya amfani jama’a wajen binciken ilimi.
An tara biliyoyin Naira a wajen taron inda Abdulsamad Rabi’u ya ba da kaso mafi tsoka na Naira biliyan 5 sai Janar Theophilus Danjuma ya biyo baya da Naira biliyan 3.