
Sakataren gwamnatin Najeriya George Akume ya bukaci ‘yan siyasar arewa su hakura da takarar shugabancin Najeriya sai 2031.
Akume wanda dan yankin arewa ne daga arewa ta tsakiya na magana ne kan zaben 2027 da ke tafe da ya ke ganin lokaci ne da ya dace a ba wa shugaba Tinubu dammar tazarce.
George a wajen taro da asusun tunawa da Sir Ahmadu Bello Sardauna da a ka gudanar a Kaduna, ya nuna ya na da kyau ‘yan siyasar arewa masu kishin kasa su hakura da batun neman shugabancin kasa a babban zabe mai zuwa.
Sakataren na gwamnati ya lissafa aiyukan alheri da ya ce gwamnatin Tinubu na gudanarwa a fadin Najeriya da baiyana cewa shugaba Tinubu ya nada ‘yan arewa da dama mukamai kuma su na taka rawar da ta dace.