
Aukawa yajin aikin gargadi da jami’an jinya wato nas-nas su ka yi, na shafar harkokin kula da majinyata.
Jami’an jinyar dai sun yanke shawarar shiga yajin aikin bayan kammalar wa’adin mako biyu da su ka bayar don biya mu su bukata amma su ka ce ba a daidaita ba.
Ba mamaki yajin aikin na gargadi ya iya kai wa har ranar 5 ga watan nan na Agusta daga nan sai jami’an su sake ba da sabon wa’adi.
Jami’an na jinya na bukatar kyautatuwar albashin su, sauran hakkoki da kuma kara daukar nas-nas don aikin ya rika zuwa cikin sauki.
Hakika ba a saba ganin jami’an jinya na wannan ajin na shiga yajin aiki ba.
Hoto-Ministan lafiya Dr.Muhammad Ali Pate