Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Gombe, Rabaran Father Joseph Alphonsus Shinga, ya ƙaddamar da wani littafi da ya rubuta domin bikin cikar sa shekaru 51 da haihuwa.
An gudanar da bikin ƙaddamar da littafin ne a cibiyar CAN da ke Gombe, a yammacin ranar Lahadi, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe, Manasseh Daniel Jatau, ɗan takarar Gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar APC, Jamilu Isiyaku Gwamna, da sauran manyan baƙi suka halarta tare da shiga aikin ƙaddamar da littafin.
Marubucin littafin mai taken “Educating for Self-Discipline and Effective Citizenship: A Philosophical Approach”, ya bayyana cewa damuwarsa kan ƙaruwar lalacewar ɗabi’a, raguwar kyawawan al’adu, tabarbarewar tarbiyya tsakanin matasa da kuma yaɗuwar cin hanci da rashawa a ƙasar nan ne suka zaburar da shi wajen rubuta littafin.
Ya ce ƙaddamar da littafin ta kuma ba shi damar gudanar da bikin cikar sa shekaru 51 da haihuwa, tare da gode wa Allah bisa kariya, alheri da arzikin da Ya yi masa.
Da yake tsokaci kan wa’adinsa na jagorantar CAN a jihar Gombe, Rabaran Father Alphonsus ya bayyana cewa riƙe wannan muƙami ya kasance wata dama ta sauyi a rayuwarsa, duk da ƙalubalen da ke tattare da shi.
Shi kuwa mai sharhin littafin, Rabaran Christopher Laima, ya bayyana cewa littafin ya ƙunshi babi biyar da suka yi bayani kan matsalolin Najeriya, musabbabin samuwarsu da kuma muhimmancin gyaran ɗabi’a da koyar da kamun kai domin gina ƙasa mafi inganci.
A nasa jawabin, ɗan takarar Gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar APC, Jamilu Isiyaku Gwamna, ya taya marubucin murnar zagayowar ranar haihuwarsa, yana mai bayyana shekarun rayuwarsa a matsayin waɗanda ya yi amfani da su wajen ayyuka masu amfani.
Ya kuma yaba wa malamin addinin bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban ƙasa ta hanyar rubuce-rubuce da kuma ƙoƙarinsa na bunƙasa kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma.
An gudanar da wasu shirye-shirye a yayin bikin, ciki har da yanke kek ɗin zagayowar ranar haihuwa, keɓe littafin da kuma addu’o’i na musamman ga ɗan takarar Gwamnan Jihar Gombe na APC, Jamilu Isiyaku Gwamna, da kuma wanda aka gudanar da bikin domin sa, Rabaran Father Joseph Alphonsus Shinga.

Leave a Reply