Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaukar sabbin sojoji 28,000 da jami’an ’yan sanda 50,000 domin ƙarfafa tsarin tsaro na Najeriya da kuma magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar ƙasar.
Amincewar na cikin shirin gwamnatin tarayya na tsara ayyukan tsaro na tsawon shekaru biyar, wanda aka tsara domin inganta ayyukan rundunonin tsaro, faɗaɗa ayyukan yaƙi da miyagun laifuffuka da kuma ƙarfafa matakan da ƙasar ke ɗauka wajen tunkarar ta’addanci, ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka.
Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Dele Alake, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce ɗaukar ƙarin sojojin zai taimaka wajen ƙara yawan jami’an soji a wuraren da ake buƙatar tsaro, inganta ƙarfin rundunar da kuma ba jami’an damar tunkarar barazanar tsaro cikin sauri da inganci.
Haka kuma, ƙarin jami’an ’yan sanda 50,000 zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron cikin gida, inganta ayyukan rundunar ’yan sanda da kuma ƙara mata ƙarfin yaƙi da miyagun laifuffuka a sassan ƙasar.
A wani mataki na ƙara ƙarfin rundunar sojin ƙasa, Shugaba Tinubu ya kuma kafa sabbin rundunonin soji guda huɗu, tare da sake fasalin wasu rundunonin da ake da su domin inganta ayyukan tsaro da tabbatar da gaggawar kai ɗauki idan wata barazana ta taso.
Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ƙasar ya amince da kafa wasu sabbin cibiyoyin horas da sojoji guda biyu a Osogbo da ke Jihar Osun, da kuma Amasiri-Edda a Jihar Ebonyi.
An tsara kowace cibiyar za ta iya horas da sabbin sojoji 6,000 a lokaci guda, wanda hakan zai sa cibiyoyin biyu su riƙa horas da sojoji 12,000 gaba ɗaya.
Sanarwar ta ce tuni aka fara horas da sabbin sojoji 5,210 a cibiyar da ke Osogbo.
Dangane da inganta walwalar jami’an tsaro da samar musu da wuraren zama, kwamitin ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da aikin gina barikin sojoji mai gidaje 700 a Ikere-Ekiti da ke Jihar Ekiti.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ya kuma yi iƙirarin cewa ayyukan soji da aka gudanar a sassan ƙasar cikin shekaru uku da suka gabata sun yi sanadin kashe ’yan ta’addan Boko Haram da ’yan bindiga sama da 15,000.
Ya kuma yi iƙirarin cewa mayaƙan Boko Haram da iyalansu sama da 130,000 ne suka miƙa wuya ta hanyar shirin Operation Safe Corridor, wanda gwamnatin tarayya ta ƙaddamar domin gyara halayen waɗanda suka tuba daga ayyukan ta’addanci.
Kwamitin ya ce shirin dabarun tsaro na shekaru biyar zai samar da tsarin da zai haɗa manufofin tsaro na ƙasa, ayyukan soji, horar da jami’ai da kuma kashe kuɗaɗen da suka dace da buƙatun tsaron Najeriya.
Ya ƙara da cewa shirin zai haɗa da ci gaba da ayyukan soji, tattara bayanan sirri, amfani da fasahar zamani da kuma matakan da ba na soja ba domin ƙarfafa tsaron ƙasa.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana takamaiman lokacin fara ɗaukar sabbin jami’an ba, ko hanyoyin neman aikin da kuma ƙa’idojin da masu sha’awar shiga aikin za su bi.

Leave a Reply