Yanzu kuma ga yadda ta kaya a duniyar Dambe. Inda a jihar Sakkwato, fafatawar ta kasance ne kamar haka:
Bahagon Mancha ya buge Bahagon Maitakwasara
Shagon Jango ya buge Dogon Musan Gyalenge
Bah Buma ya kashe BH. Ramadan
Shagon na dada ya buge Autan Hasan Kalallagi
A Kano kuwa:
Wurkilli ya sumar da shagon Babba, inda ya sumar da shi da mangare, kamar yadda yayi mashi a makon da ya gabata.

Aljanin Nokia da shagon Guramada, babu kisa a wasan.
Yayinda a jihar Nasarawa (gidan damben Maraba), shi kuwa Burin Sola na Autan dan Bunza ya cika, inda aka hada shi da Manu shagon garkuwan cindo wanda yace ya daɗe ya na fatan ta haɗa su sabida ya taɓa buge Maigidan shi wato Autan Dan Bunza.
Sai kuma Bagobirin Guramaɗa zai fafata da Autan Auta daga ɓangaren Jamus.
Sai Dogon Dogo Maitakwasara za su kece raini da ayi kullum daga ɓangaren Jamus, akan gasar nair dubu dari 3, duk a Maraba a ranar Lahadi mai zuwa.


