Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

An Gudanar Da Zanga-Zanga A Guinea-Bissau
Published: December 12, 2025 at 8:05 PM | By: Bala Hassan | Updated: December 12, 2025

Daruruwan mutane sun yi macin yau jumma’a a titunan babban birnin Guinea-Bissau, domin nuna rashin jin dadinsu da juyin mulkin da aka yi a watan da ya shige, tare da neman a sako shugabannin hamayya da aka kama aka tsare.

Masu zanga zanga sun yi arangama da dakarun tsaro a Bissau a yayin da suka toshe hanyoyi ta hanyar kona tayu da kuma yin kiran da a sako Domingos Pereira, shugaban jam’iyyar hamayya wanda aka kama a lokacin juyin mulkin.

Hafsoshin soja sun hambarar da shugaba Umaero Sissoco Embalo a ranar 26 ga watan nuwamba, kwana daya kafin hukumar zabe ta kasar ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi.

Sojojin sun nada manjo janar Horta Inta-a a matsayin shugaban kasar na wucin gadi.

A yayin da wannan ke faruwa ne kuma shugabannin kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yankin na Afirka ta yamma, ECOWAS, suke shirin ganawa a Abuja, babban birnin tarayyar Naeriya domin tattauna lamarin na kasar Ginea-Bissau, tare da nazarin kafa mata takunkumi.

Afrika

Post navigation

Previous Post: Messi Da Cristiano Suna Da Tasiri A Gasar Cin Kofin Duniya 2026
Next Post: Akalla Mutane 8 Sun Mutu Biyo Bayan Bindiga Da Wata Tanka Tayi

Karin Labarai Masu Alaka

Bisa Alamu Hadinkan Kasashen Yankin Sahel Zai Haifar Da Nagarta Afrika
Shari’ar Ta’addanci: Manyan Jagororin Ansaru Biyu Sun Amsa Laifi A Abuja Afrika
Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika
An Kara Wa’adin Zaman Kurkuku A Senegal Ga Masu Auren Jinsi Afrika
‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji A Kauyen Wanka Jihar Filato Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kamfanin Bitcoin A Korea Ta Kudu Yayi Kuskuren Turawa Masu Mu’amala Da Kamfanin Kudade Afrika
  • UNICEF Ta Tallafawa Jihar Bauchi Da Babura Afrika
  • Yan Najeriya na ci gaba da maida martani akan sabuwar dokar zabe da majalisar Dattawan kasar ta Amince dashi Najeriya
  • Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami Afrika
  • Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya Labarai
  • Pantami Ya Bayyana Dalilin Mayar Da Zaben Sa Abuja Afrika
  • Tantance Gaskiyar Bayanai Shi Ne Ginshiƙin Aikin Jarida Mai Nagarta – Abdulaziz Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.