A fafatawar jihar Kano tsakanin Alhasan na ɓangaren Jamus da Wurƙilili na ɓangaren kudu, wasan ya baiwa kudawa ruwa, domin kuwa Alhasan ɗin ya yi nasarar kifar da Wurƙilili a naushin rugu-rugo da akayi.
Alhasan dai da Junior Ramadan sun koma gidan Damaben jihar Kano ne bayan shafe tsawon lokaci suna fafata wasa a jihar Nasarawa.
A ɓangare guda kuma, Wasan da aka fafata na Damben kuɗi a jihar Katsina, Bahagon Ali Kansila ƙarami ya buge dogon Bahagon musan Kaduna ne turmin farko na gasar da aka gwabza a yammaci ranar Asabar 13 ga watan Disambar, 2025. Shima Bahagon Yahaya Tarasa ya buge Bahagon Abban Nabacirawa a turmi na biyu duk a Damben gasar jihar Katsina.
A gobe Lahadi 14 ga watan Disamba ne ake sa ran fafatawar nan da ake ta burin ganin a jihar Nasarawa, tsakanin: Manu daga ɓangaren Guramada da kuma Sola daga Jamus, sai kuma Autan Auta daga ɓangaren Jamus sai kuma Bagobirin Guramada da Kuma Ayi Kullum da Dogon Dogo.


