Shugaba Vladimir Putin na Rasha, yace wasu shawarwarin dake kumshe cikin shirin Amurka na kawo karshen yakin Ukraine, ba masu karbuwa ba ne ga kasarsa, abinda ke nuna cewa har yanzu da sauran aiki kafin a iya cimma yarjejeniya.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya kaddamar da yunkurin diflomasiyya mafi girma da aka gani na kawo karshen yakin tun lokacin da Rasha ta kaddamar da hari kan makwabciyarta kusan shekaru hudu da suka shige.
Putin ya ce tattaunawar da yayi da wakilin Amurka Steve Witkoff da surkin shugaba Trump, Jared Kushner, suna da amfani, amma kuma mawuyaciya ce, kuma wasu shawarwarin ba zasu karbu ga Rasha ba.
Da yake magana da gidan telebijin na India Today a ranar alhamis kafin ya sauka a New Delhi don fara ziyarar aiki a kasar Indiya, shugaba Putin yace shawarwarin da aka tattauna a kansu a fadar Kremlin, sun samo asali ne daga tattaunawar Rasha da Amurka da kuma tattaunawar da yayi da shugaba Trump a Aaska, amma kuma sun kumshi wasu sabbin shawarwarin.
Yace sai da suka bi kowace shawara daya bayan daya, abinda ya sa tattaunawar tasu ta yi tsawo ke nan.
Shugaba Trump ya fada a ranar laraba cewa Witkoff da Kushner sun fito daga tattaunawar da kwarin guiwar cewa lallai shugaba Putin na Rasha yana son a cimma yarjejeniyar zaman lafiya.


