Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Amurka Na Shirin Kauracewa Taron Kungiyar Kasashen G20
Published: November 21, 2025 at 4:36 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Fadar shugaban Amurka ta White House ta musanta kalamun da shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika Ta Kudu (ATK) yayi jiya Alhamis inda yake cewa Amurka tana tunanin canja ra’ayinta game da kauracewa taron kolin kasashen kungiyar G20 a birnin Johannesburg.

A wajen wani taron manema labarai da manyan jami’an Kungiyar Tarayyar Turai jiya alhamis, shugaba Ramaphosa yace sun samu wata sanarwa daga Amurka game da canja ra’ayi ko kuma dai halartar taron a wani matsayi.

Wata jami’ar White House ta musanta wannan, tana mai cewa karamin jakadan Amurka dake Pretoria zai je wurin taron ne domin karbar ragamar jagorancin kungiyar na karba-karba wanda zai komo hannun Amurka, amma ba wai don halartar wani abu na taron ba.

Gwamnatin shugaba Trump ta ce Amurka ba zata halarci taron farko na kungiyar G20 da za a yi a Afirka ba, tana mai zargin cewa ATK mai masaukin baki, wadda turawa ‘yan tsiraru na kasar suka mulke ta har zuwa 1994, tana gallazawa da cin mutuncin turawan kasar.

Ita dai kungiyar ta G20, kungiya ce ta kasashe 19 da suka kunshi wadanda suka fi arziki da kuma wadanda tattalin arzikinsu ke tasowa sosai. A shekarar 2023, KTT da KTA, sun shiga a zaman membobi masu wakiltar kasashensu, kungiyar ta zamo mai membobi 21.

Wannan kungiya, ba kamar kungiyar G7 ta kasashe mafiya arziki zalla ba, tana mayarda hankulanta ne kan tattalin arzikin duniya da ayyukan raya kasa. Sai dai kungiyar ba ta da hedkwata, kuma ba ta cimma shawarwarin da dole membobi suyi aiki da su, abinda ya sa masu sukar lamiri suke ce kungiyar haushi kawai ta iya, ba ta da hakoran yin cizo.

Afrika

Post navigation

Previous Post: Shirin Dare 2030 UTC Yau Alhamis 11.20.2025
Next Post: Ba Shakka Najeriya Zata Iya Shiga Gasar Harbi Ta Duniya

Karin Labarai Masu Alaka

Prime Ministan Senegal Ya Bayyana Shirin Sauya Sheka Afrika
ECOWAS Da AU Sun Nuna Damuwa Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau Afrika
CHAN Ta Duba Lafiyar Idanun ‘Yan Jarida A Filato Afrika
‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Cin Karensu Babu Babbaka A Najeriya Afrika
Jami’an Tsaro Suna Farautar Wasu ‘Yan Ta’adda A Najeriya Afrika
Birtaniya Zata Hana Jiragen Ruwan Rasha Wucewa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Malaman Makaranta A Tilabery Afrika
  • Fargaba Ta Karu Duk Da Tsagaita Wuta Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
  • Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Bukaci Samar Da Zaman Lafiya A Filato Afrika
  • Gwamnatin Jihar Kano Zata Kashe Makudan Kudade Ga Jama’ar Kano! Najeriya
  • Ƙungiyoyin Premier 17 Za Su Rasa ‘Yan Wasa 40 saboda Gasar AFCON 2025, Wasanni
  • Ukraine Zata Sayi Iskar Gas Daga Mozambique Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Sarakunan Gumel Da Zurmi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.