An kashe ‘yan ta’adda yayin da sojoji suka dakile hari kan sansanin soja a Borno.
Dakarun Rundunar Operation HADIN KAI (OPHK) sun dakile wani hari da ‘yan ta’addan ISWAP suka kai wa Sansanin Sojoji na Gaba (FOB) a Mairari a Jihar Borno, inda suka tarwatsa motocin bama-bamai guda biyu (VBIEDs) da aka yi yunkurin amfani da su wajen kutsawa sansanin.
A cewar Jami’in Yada Labarai na OPHK, Laftanar Kanal Sani Uba, harin da ya faru a daren Juma’a an dakile shi ne ta hadin gwiwar hare-haren kasa da na sama, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda da dama, yayin da wasu suka jikkata.
Bayan harin, sojoji tare da hadin gwiwar ‘yan sanda da CJTF sun gudanar da bincike a yankin, inda suka kwato makamai, harsasai, gurneti, babura da kayayyakin yaki da ‘yan ta’addan suka bari.
Uba ya ce ‘Yan ta’addar basu sami nasarar kutsawa sansanin ba, kuma a halin yanzu dakarun na ci gaba da sintiri domin hana sake kai hare-hare da tabbatar wa al’umma tsaro.


