Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Hafsan Sojin Najeriya: Samar Da Sabbin Wajen Horas Da Sojoji Zai Inganta Tsaro
Published: December 14, 2025 at 4:13 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar-Janar Shaibu ya yaba, ya ce buɗe sabbin cibiyoyin horas da kuratan sojoji a jihohin Kudu zai ƙara ƙarfin rundunar wajen daukar dakaru a faɗin ƙasar.

‎Laftanar-Janar Shaibu ya tuna cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sahale buɗe sabuwar cibiyar horas da sabbin kuratan sojojin ne a Abakaliki da ke Jihar Ebonyi.

‎‎Ya kara da cewa a mako mai zuwa Depot na Abakalaki da kuma na Osogbo da ke Jihar Osun za su yaye sabbin kuratan sojoji da suka kammala horaswa.

‎‎Ya bayyana haka ne a yayin bikin yaye sabbin dakarun soji 3,439 da aka yi a Cibiyar Horas da Sabbin Kuratan sojoji da ke Zariya, inda ya shawarce su da su zama masu kishin ƙasa da jajircewa.

‎‎Ya taya sabbin sojojin murnar kammala horon farko na soja, wanda ya ce, shi ne matakin farko na doguwar tafiyar sadaukarwa, kishin ƙasa, da hidima ga al’umma.

‎A karshe, Laftanar-Janar Shaibu ya bayyana ranar a matsayin ranar nuni da babban ci gaba wajen cika manufar rundunar sojojin Najeriya ta faɗaɗa karfin ma’aikata.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Jihar Gombe Tayi Fice A Bangaren Inganta Lafiya Matakin Farko
Next Post: Gwamnatin Kano Ta Samar Da Wasu Dabarun Inganta Tsaro

Karin Labarai Masu Alaka

Mayakan RSF A Sudan Suna Sace Kananan Yara A Lokacin Yake-Yaken Kasar Afrika
Rundunar Operation Hadinkai Sunyi Nasara Akan ISWAP Da Boko Haram Najeriya
Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika
Isra’ila Ta Zantar Da Hukuncin Kisa Ga Masu Kai Hare Hare Labarai
Shugaban Amurka Ya Ya Bukaci Iran Ta Mika Wuya Afrika
Iran Ta Tsagaita Kai Hare Hare Makwabta Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu Ya Nuna Alhinin Rasuwar Janar Rabe Abubakar, Ya Jajanta wa Iyalansa Afrika
  • Babu Dabbar Da Zata Sake Shiga Amurka Daga Mexico! Amurka
  • Malami: “Da Gwamnatin Tarayya Na Daukar Shawara Da Ba’a Kai Inda Ake Ba” Najeriya
  • AIG Kwaimo Ya Kai Ziyarar Aiki Gombe, Ya Buƙaci Ƙara Ƙaimi A Yaƙi Da Ta’addanci Labarai
  • Sarkin Musulmi Yayi Magana Game Da Matsalar Tsaron Kasar Tsaro
  • Sabuwar Sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Za Ta Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaban Yankin Afrika
  • Mutane 13 Sun Mutu Inda Wasu 57 Suka Jikkata A Barundi Afrika
  • Majalisar Dattawa Ta Wanke Janar Christopher Musa A Matsayin Minista Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.