Najeriya ta dauki kwngilar wani kamfani masu aikin kama kafa, da ake kira “Lobbyist” da turanci, kan kudi dala milyan tara a shekara, domin ya kyautata dangantarta da gwamnatin shugaba Trump. Kamfanin mai suna DCI group, zai yi aikin karyata zuki ta malle da kasar tace wasu kungiyoyin addinin kirista da wasu mutane suke yadawa cewa gwanatin ta gaza kare su.
Domin wannan zargin ne, shugaban Amurka Donald Trump, cikin watan Nuwamaban bara, ya ayanna Najeriya cikin “jerin kasashe da Amurka take da damuwa akan su.” lamarin da ya kai ga barazanar daukar matakin soja, idan kasar batayi wani abu kan kashe kiristoci ba. Saboda haka ne Amurkan ta kaddamar da wani hari ranar kirstimeti, wadda Trump yace an auna mayakan sakai dake ikirarin Islama.
Bayanan yarjejenyar da Najeriya ta kulla da kamfanin DCI, yana kunshe ne cikin bayanai da kamfanin ya baiwa gwamnati ranar 18 ga watan jiya, kamar yadda ma’aikatar shari’a ta Amurka ta bayyana a shafinta na Internet.
Nan take dai fadar gwamnatin Najeriya bata ce uffan ba da ak nemin jin ta bakinta kan wannan batu.


