A yau Alhamis, Amurka tayi barazanar zata rage tallafin da take baiwa Sudan ta kudu, muddin kasar bata janye abunda ta kira haramtacciyar haraji da kasar ta aza kan kayayyakin jinkai da ake aikawa ksar ba.
A cikin wata sanarwa na ba sai fa, daa aka yiwa lakabin “A daina cin zalin Amurka” cibiyar kula da harkokin Afirka ta Amurka, ta zargi Sudan ta kudu da tsawwala kudin haraji kan kayayyakin jinkai, tare da hana MDD tafiyar da ayyukan kiyaye zaman lafiya.
Amurka wacce a bana ta rage yawan tallafin da take baiwa kasashen ketare, itace kasar data fi ko wacce tallafawa Sudan ta kudu. Kasar mai mutane milan 12, yaki ya daidaita kasar tun bayann da ta sami ‘yancin kai daga Sudan a 2011.
Kasashe da suke bada tallafi, suna turjiya ga yunkurin hukumomn Sudan ta kudu na neman su karpi haraji kan tallafi da suke aikewa kasar.
Ministan kula da harkokin jinkai na Sudan ta kudu, bai maida martani nan take ba, da aka nemi jin ta bakinsa.
Ahalinda ake ciki kuma, Sudan ta kudu tace ta tura sojojinta zuwa makwabciyarta Sudan domin gadin rijiyoyin mai dake kan iyakokin kasashhen biyu, kamar yadda hafsan sojojin kasar ya fada yau Alhamis, kwanaki bayanda sojojin wucin gadi na Sudan da ake kira RSF suka bada sanarwar cewa sun kama yankin da rijiyoyin man suke.


