An samu hayaniya a rangadin da fittacen dan wasan kwallon kafa na duniya Lionel Messi ya kai a Indiya.
Rangadin Lionel Messi a Indiya ya fara ne da rudani a ranar Asabar yayin da magoya baya suka balle kujeru suka jefa cikin filin wasa bayan ɗan gajeren ziyarar da ya kai filin wasa na Salt Lake da ke Kolkata.

Messi ya je Indiya ne a wani ɓangare na rangadin wanda aka shirya zai halarci asibitocin ƙwallon ƙafa na matasa, a taron gasar Padel da kuma ƙaddamar da ayyukan agaji a Kolkata, Hyderabad, Mumbai da New Delhi.

A cewar rahotannin da kafofin watsa labarai na Indiya suka bayar, wanda ya lashe gasar cin kofin duniya ta 2022 ya yi yawo a filin wasa yana daga wa magoya baya hannu, amma an kewaye shi da gungun mutane na mintuna 20 bayan isowarsa.
A wata Bidiyon an nuna magoya baya suna jefa kujerun filin wasa da sauran wasu abubuwa, yayin da mutane da dama suka hau kan shinge da ke kewaye da filin wasa suna jifa abubuwa.

Daga farko dai an shirya Messi zai ziyarci filin wasa na mintuna 45, ne amma bayyanarsa ta ɗauki mintuna 20 kacal.
An fara sayar da tikitin shiga taron daga kusan rupees 3,500, kudin Indiya kimanin Dala ($38.65) – wadda tafi fiye da rabin matsakaicin kuɗin shiga na mako-mako a Indiya – amma wani mai goyon baya ya ce ya biya dala $130 (£99).
“Jagororin da su shirya taron ne kawai kewaye da Messi… Me ya sa suka kira mu a lokacin? Mun sayi tikitin rupees 12,000 [$132.51, £99], amma ba mu ma ga fuskarsa ba,” in ji wani wanda ya biya kudin sa don yaga Messi.
Masu shirya rangadin Messi a Indiya ba su amsa nan take ga buƙatar tsokacin da akayi ba, amma ‘yan sanda sun tsare Satadru Dutta, babban mai shirya taron, in ji Rajeev Kumar, babban daraktan ‘yan sandan West Bengal.
Kumar, ya shaida wa manema labarai: cewar an tsare babban mai shirya taron, ana ɗaukar mataki ya ya yi alƙawarin a rubuce cewa ya kamata a mayar da tikitin da aka sayar don taron.”
Babban ministan West Bengal, Mamata Banerjee, ta nemi afuwa ga Messi sannan ta ba da umarnin a gudanar da bincike kan lamarin.


