Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika

Marc Brys: “Eto’o Baiyi Adalci Ga Onana, Da Vincent, Ba”
Published: December 7, 2025 at 9:39 PM | By: Bala Hassan | Updated: December 8, 2025

­Tsohon kocin Kamaru Marc Brys ya zargi shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kamaru (FECAFOOT) Samuel Eto’o­, da tsoma baki a zaben ‘yan wasan Indomitable Lions da za su fafata a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta 2025,

Brys, wanda aka kora makonni kadan kafin fara gasar da aka tsara daga 21 ga Disamba zuwa 18 ga Janairu, ya yi ikirarin cewa Eto’o ne yake Zaben ‘Yan wasa ba sabon kocin da aka nada David Pagou ne ya dauki nauyin tsara jerin ‘yan wasa na karshe ba.

Kocin dan kasar Belgium ya soki cire manyan taurari, ciki har da mai tsaron gidan Manchester United André Onana da kyaftin dinsa Vincent Aboubakar na dogon lokaci, yana mai bayyana ceresu a matsayin rashin adalci da kuma illa ga damar Kamaru a gasar.

Abubakar shi ne na biyu mafi yawan kwallaye a tarihin kungiyar kwallon kafa ta kasar, inda ya zura kwallaye 45 a wasanni 116.

“Eto’o ya cire manyan ‘yan wasa, kuma Jagorori, domin ya sa ka wanda yake so wannan a bayyane yake “in ji Marc.

Marc ya ce ta yaya za ku iya shiga gasa irin wannan ba tare da mai tsaron gida sananne a duniya ba, ko kuma ba tare da Aboubakar ba?

Waɗannan ‘yan wasa ne masu kwazo, waɗanda ke tsayawa tsayin daka ” in ji Brys a wata hira da wata kafar yada labarai

Brys ya ƙara da sukar halayen Eto’o, yana zargin tsohon ɗan wasan Barcelona da Inter Milan da cewa mai son kai ne.

“Duk wannan ba abin mamaki ba ne a gare ni wajan wanda ke son kai kuma yana tunanin shi ne ya Iya ,” in ji shi.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Masana: ‘Yancin Kasashen Afrika A Rubuce Yake Ba A Zahirance Ba
Next Post: Tinubu: Sojojin Mu Sun Yi Rawar Gani Don Kare Demokuraɗiyya A Jamhuriyar Binin

Karin Labarai Masu Alaka

Wasu Zakaru Da Suka Samu Karramawar Hukumar CAF Ta Afrika Wasanni
Yan Fashi Sun Shiga Gidan Alex Iwobi A Ingila Wasanni
AFCON 2025, Jerin Abubuwan Da Aka Haramta Wa Magoya Baya Wasanni
Salmanu: Ci Gaban Wikki Tourist FC Shine A Gaba Na Wasanni
An Dakatar Da Daniel Bisa Zargin Fyade Wasanni
Kocin Zambia Na Mata Ba Lafiya Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka Afrika
  • An Kubutar Da Wani Wanda Mahaifinsa Ya daure Da Sarka Tsawon Shekaru 17 A Bauchi Labarai
  • An Kubutar Da ‘Yan Matan Sakandire Su 24 Na Jihar Kebbi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta Kimiya
  • Kasar Sham Ta Sanar Da Tsagaita Wuta Tsakaninta Da Kungiyar Kurdawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Zata Bada Gudunwa Ga Masu Zanga-Zanga A Iran Sauran Duniya
  • Kungiyar HPV A Jihar Gombe Ta Jagoranci Yaki Da Karuwar Cutar Daji Afrika
  • Kamfanin Bitcoin A Korea Ta Kudu Yayi Kuskuren Turawa Masu Mu’amala Da Kamfanin Kudade Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.