Farashin mai yaci gaba da tashi a yau Talata, yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya ci gaba da tsaurara maganar sa kan Iran, inda yayi barazanar daukan mataki mai tsanani idan taki bude mashigin ruwa na Hormuz.
Man Brent crude futures ya tashi da kashi 0.5 cikin dari, inda kowacce ganga ta kama kan dala 110.34, yayin da nau’in man West Texas Intermediate shi kuma ya tashi da kashi 1.1 cikin dari, kowacce ganga a kan dala 113.67.
Trump yayi barazanar luguden wuta kan Tehran idan Iran bata bude mashigin ruwan Hormuz ba zuwa wa’adin da ya bayar na karfe 8:30 na daren yau Talata. Iran kuma taki yarda da yarjejeniyar tsagaita wuta, tace wajibi ne a kawo karshen yakin gabaki daya.


