Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya zabi wani tsohon babban Hafsan Sojoji ya maye gurbin ministan tsaron Kasar wanda yayi murbus jiya Litinin, a lokacin da akasami karin sace sacen mutane, da hare haren ‘yan ta’addar dake ikirarin Musulunci a Arewacin Kasar, lamari da ya kai ga shugaban kasar ayyana dokar tabaci.
Dan shekaru 58 da haifuwa, Janar Christopher Musa, ya rike mukamin babban Hafsan mayakan Najeriya daga 2023 zuwa watan oktobann bana. Zai maye gurbin Mal Badaru Abubakar tsohon gwamna daga Arewacin Najeriya, wanda yayi murabus, bisa dalilan rashin koshin lafiya.
Shugaba Tinubu ya bada sanarwar nadin ne, a cikin wasika da ya aike wa majalisa, kamar yadda ofishinnsa ya fada.
Wannan nadin yana zuwa ne ‘yan kwanaki kacal, bayan da shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci, a zaman martani ga karin tashe tashen hankula a kasar.
Har yanzu ba’a gano dalibai su sama da maitan da ‘yan bindiga suka sace a wata makarantar darikar Katolika ranar 24 ga watan nuwamban nan data kare. Suna daga cikin akalla mutane 402 da aka sace a kasar daga tsakiyar watan Nuwamba, kamar yadda MDD ta bayyana.


