Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure
Published: February 4, 2026 at 2:23 PM | By: Bala Hassan | Updated: February 5, 2026

Kotu ta yanke hukuncin kisa ga barawon da ya kashe Mai Babur a hanyar Estate a jihar Bauchi dake Arewa maso gabas a Najeriya.

Babban Kotun Jihar Bauchi mai lamba hudu, karkashin jagorancin Mai Shari’a Aliyu Baba Usman, ta yanke wa wani mutum mai suna Mamuda Zakariyau hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe wani mai babur, ta hanyar daba masa wuka, lokacin da ya yi yunkurin satar babur dinsa.

Da yake yanke hukuncinsa a Bauchi, Alkali Aliyu ya ce “Saboda kotu ta sameka da aikata laifin kisan, wanda hukuncinsa kisa ne, wanda ake tuhuma Mamuda Zakariyau an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya”.

Da yake gabatar da karan a kotu, Lauyan Ma’aikatar Shari’a, Yusuf Adamu ya bayyana tuhuma guda biyu akan wanda ake tuhuma.

Yace a ranar 16/10/2026, Mamuda ya hada baki da Sadiq wanda aka fi sani da Gwaska wanda yanzu haka ana nemansa ba’a sameshi ba, sun hau babur din wani mutum mai suna Basiru Mohammed wanda yake tuka babur din, suka hau akan ya kaisu zuwa tsohon filin jirgin sama, da suka isa sai ya zaro wuka ya daba masa, suka yi masa fashin babur, aikata hakan kuma ya sabawa, sashe na 1(2) kan fashi da makami na dokar musamman mai lamba LFN 2004 na aikata fashi da makami”.

Tuhuma ta biyu lauyan yace Mamuda ya hada baki da Sadiq wanda aka fi sani da Gwaska, suka aikata laifin kisan kai lokacin da suka daba wa Basiru wuka suka kuma yi masa fashin babur, wanda hakan ya sa ya fadi ya mutu a wajen sakamakon sukansa da akayi da wuka, aikata laifin kisan kai dai ya saba wa sashe na 217 na dokar Penal Code ta jihar Bauchi.”

Mai gabatar da kara ya kira shaidu hudu kuma ya gabatar da shaidu biyar da suka hada da wayar hannu, babur, wuka da jini ajiki, da takalma.

Lauyan wanda ake kara, Barista Kayode Omosehin, ya nemi kotu da ta wanke wanda ake kara daga aikata laifi, saboda ikirarin da aka yi na cewa ya aikata laifi, ya saba wa tsarin dokokin shari’a na jihar Bauchi, kuma babu shaidun da suka gani da idonsu lokacin da ya aikata laifin .”

A cikin hukuncinsa, Alkali Aliyu Baba Usman ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da cewa dukkan tuhume-tuhumen da suka gabatar akan wanda ake kara sun tabbata, wanda ake kara Mamuda Zakariyau an same shi da laifin fashi da makami, sabanin sashe na 1(2) na dokar fashi da makami mai lamba Cap R 11 LFN 2004 an Kuma sameshi da aikata laifin kisan kai wanda hukuncinsa kisa ne sabanin sashe na 217 na dokokin PC na jihar Bauchi.”

Idan Za ku tuna kwanaki cikin watan Oktoba 2025, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekaru 30, Mamuda Zakari Yau, bisa zargin daba wa wani mai babur wuka har lahira da kuma satar babur dinsa a wani yunƙuri na neman kuɗi don ya kara aure.

An yi zargin cewa Mamuda ya yi amfani da wuka ya daba wa Mohammed Basiru Mai Babur, Sai ya fadi ya Mutu, sannan ya tafi da babur ɗinsa mai launin ja na Bajaj Boxer, mai lambar rajista NNG 813 UM.

“Sai dai Bayan an sokeshi da wuka Shi wanda aka kashe kafin yafadi yayi kururuwa yana neman taimako, wanda hakan ya jawo hankalin mazauna kusa. Wasu mutane suka bi wanda ake zargin, inda suka tilasta masa barin babur ɗin ya gudu, ya buya, yan sanda da ke Yelwa sunje wurin da lamarin ya faru.

Suka garzaya da wanda aka kashe zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsaa, sannan daga baya an gano wanda ake zargin kuma an kama shi bayan bayanan sirri da aka tattara daga wayarsa ta hannu da aka gano.

“A lokacin da ake mass tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin kuma ya yi iqirarin cewa ya aikata laifin ne saboda takaicin kuɗi, yana mai cewa yana buƙatar kuɗi don ya auri mata ta uku”.

“Ya yarda cewa ya yaudari mai babur ɗin kafin ya daba masa wuka ya sace masa babur ɗinsa,” Kuma kayayyakin da aka samu daga wanda ake zargin sun hada da babur kirar Bajaj Boxer ja, wuka mai jini, takalma, da kuma wayar Android guda daya mallakarsa.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Gombe Ta Kulla Yarjejeniyar Da New Zealand
Next Post: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Kauyuka Dake Yammacin A Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Ferfesa Pantami Yasamu Tikitin Takarar Gwamnan Gombe A Jami’yar PDP Afrika
Hawan Gidan Gwamnati A Jihar Gombe Afrika
Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Afrika
Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Bukaci Al’ummar Gombe Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Ta’addanci Afrika
Farashin Mai A Kasuwannin Duniya Yayi ƙasa Kadan Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Amurka Zata Fice Daga Iran Cikin Gaggawa Afrika
  • Ba Mamaki APC Ta Kafa Tarihi A Ranar Litinin Najeriya
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
  • Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Guinea Bissau Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya Labarai
  • Farashin Danyen Mai Ya Farfado Fiye Da Kashi Daya Sauran Duniya
  • Sojojin Amurka Sun Kashe Wasu Fararen Hula Ba Dalili Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.