Shugaba Donald Trump na Amurka ya fada cewa shi da shugaba Volodymyr Zekensky na Ukraine sun kara gusawa ga cimma daidaituwa a kan yarjejeniyar kawo karshen yakin Ukraine, amma kuma yace har yanzu ba a cimma matsaya guda ba, a kan muhimmin batun nan na makomar yankin Donbas ba.
Shugabannin biyu sun yi magana a taron ‘yan jarida na hadin guiwa bayan tattaunawarsu a gidan shugaba Trump na Mar-a-Lago dake jihar Florida.
Shugabannin biyu, sun ce an samu ci gaba a kan wasu muhimman batutuwa biyu masu sarkakiya, watau tabbatar da tsaron kasar Ukraine da yadda za a raba yankin Donbas na gabashin ukraine, yankin da Rasha ke neman mallaka baki dayansa.
Trump yace nan da ‘yan makonni kadan za a san ko za a iya cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
Zelensky yace an cimma yarjejeniya a kan batun tabbatar da tsaron kasar ukraine a nan gaba, watau ba kasar Garanti na tsaro daga duk wani harin Rasha ko wata kasa amma shugaba Trump ya nuna taka tsantsa kan wannan batu, yana mai fadin cewa an cimma kashi 95 cikin 100 ne a batun ba kasar ta ukraine garanti na tsaro.
Yace ana sa ran kasashen Turai zasu dauki alhakin wannan tare da goyon bayan Amurka.


