Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya wato (INEC) ta ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027, inda Shugaban Hukumar, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya jagoranci tawagar manyan jami’an hukumar zuwa Jihar Gombe domin tantance matakin shirye-shiryen gudanar da zaɓe a jihohin Arewa maso Gabas guda shida.
Ziyarar tantancewar ta haɗa da Kwamishinonin Ƙasa na hukumar, Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi (RECs) daga jihohin yankin da sauran manyan jami’ai, inda suka tattauna da jami’an da za su gudanar da ayyukan zaɓe a matakin jihohi da ƙananan hukumomi domin gano ƙalubale da hanyoyin inganta shirye-shiryen zaɓen.
Da yake jawabi a yayin taron a Gombe, Farfesa Amupitan ya ce ziyarar wani ɓangare ne na shirin hukumar na zagayawa sassan ƙasar domin tantance shirye-shiryen ma’aikata, gano matsalolin da za su iya kawo cikas da kuma ƙarfafa shirye-shiryen gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.
Ya bayyana cewa zagayen tantancewar ya fara ne a Legas a ranar 7 ga Satumba, 2026, domin duba yankin Kudu maso Yamma, kafin ya wuce Kaduna a ranar 28 ga Satumba domin yankin Arewa maso Yamma, sannan Enugu a ranar 20 ga Oktoba domin Kudu maso Gabas, daga bisani kuma Gombe a ranar 26 ga Oktoba domin tantance Arewa maso Gabas.
Shugaban INEC ya jaddada cewa sahihancin zaɓe ba ya dogara da tarurrukan manyan jami’ai a ofisoshi kawai, sai dai yana farawa ne daga yadda jami’an zaɓe suke gudanar da aikinsu a filin aiki.
“Gaskiyar zaɓe ba ta tabbata a ɗakunan taro masu sanyaya iska a Abuja ba; a fagen aiki ake tabbatar da ita,” in ji shi.
Ya ce ingancin zaɓe yana da alaƙa da shirin jami’ai, ingancin kayan aiki, kasancewar kayayyakin more rayuwar da ake buƙata da kuma kyakkyawan haɗin gwiwa tsakanin sassan hukumar.
Farfesa Amupitan ya bayyana cewa yankin Arewa maso Gabas yana da masu rajistar zaɓe 13,965,475, waɗanda suke wakiltar kashi 13.51 cikin 100 na jimillar masu rajistar zaɓe sama da miliyan 103 a Najeriya.
Ya ce hukumar na ci gaba da aikin tantancewa da tsaftace bayanan rajistar zaɓe bayan kammala aikin ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR).
A jawabinsa na maraba, Kwamishinan Zaɓe na Jihar Gombe, Mukhtar Gajiram Umar, ya bayyana tsarin zaɓe na jihar da kuma matakan da hukumar ke ɗauka domin tabbatar da shirye-shiryen zaɓen 2027.
Umar ya ce Jihar Gombe tana da mazabun Sanatoci uku, mazabun Majalisar Wakilai ta Tarayya shida, mazabun Majalisar Dokokin Jiha 24, yankunan rajista 114 da rumfunan zaɓe 2,988.
Ya ce bayan kammala aikin ci gaba da rajistar masu zaɓe, jihar tana da masu rajistar zaɓe 1,768,566, kafin kammala aikin tantance bayanan rajistar ta hanyar na’urar Automated Biometric Identification System (ABIS).
Kwamishinan ya ƙara da cewa tun bayan buɗe shafin INECPRES, an fara ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi da za su taimaka wajen gudanar da zaɓe, yayin da aka fara shirye-shiryen horas da jami’an zaɓe daban-daban.
Ya kuma bayyana cewa sashen fasahar sadarwa da rajistar masu zaɓe ya fara gwaje-gwajen fasaha kan na’urori da kayayyakin more rayuwar da ake buƙata domin zaɓen 2027.
A cewarsa, wannan mataki zai taimaka wajen gano matsalolin fasaha tun da wuri, tantance yanayin kayan aikin zaɓe da tabbatar da cewa kayayyakin sadarwa da fasahar zamani za su kasance cikin shiri kafin ranar zaɓe.
Tsaro da ƙwarewar ma’aikata
Dangane da matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan Arewa maso Gabas, Shugaban INEC ya ce kare rayukan masu zaɓe, jami’an zaɓe da masu sa ido kan zaɓe yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sahihancin zaɓe.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro ta hanyar Kwamitin Tuntuɓar Hukumomi Kan Tsaron Zaɓe (ICCES) domin tsara matakan tsaro da za su ba da damar gudanar da zaɓe cikin lumana.
Amupitan ya buƙaci jami’an zaɓe su san tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026, ƙa’idoji da jagororin gudanar da zaɓe na 2026 da kuma sauran kundin tsarin ayyukan hukumar.
Ya kuma gargaɗe su da su kasance masu tsaka-tsaki da ƙwarewa, su guji matsin lambar siyasa, cin hanci, barazana da nuna bambanci na ƙabila, tare da tabbatar da cewa an rubuta bayanan dukkan ayyukan zaɓe yadda ya kamata.
Daraktar Tsare-tsare da Sa-ido ta hukumar, Helen Ajayi, ta ce manufar tantancewar a matakin shiyya ita ce gano matsayin shirye-shiryen kowace jiha da kuma matsalolin da za su iya kawo cikas ga gudanar da zaɓen 2027.
Ta ce taron zai kuma ƙarfafa bin ƙa’idojin ɗabi’a na hukumar da tabbatar da cewa kowane jami’i ya fahimci nauyin da ke kansa kafin zaɓe.
A yayin taron, daraktoci da wakilan sassan wayar da kan masu zaɓe da yaɗa bayanai, rajistar masu zaɓe, fasahar sadarwa, kula da ma’aikata, da gudanar da zaɓe sun gabatar da bayanai kan shirye-shiryen da ake yi a sassansu.
An bayyana ranakun zaɓen 2027
A yayin jawabin nasa, Farfesa Amupitan ya bayyana cewa an tsara gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan Majalisar Dokokin Tarayya a ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan Majalisun Dokokin Jihohi a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
Ya ce hukumar tana da ɗan lokaci kaɗan na kammala shirye-shiryenta, don haka ya buƙaci ma’aikata su ƙara himma da mayar da hankali wajen gudanar da ayyukansu.
Ya bayyana cewa gyare-gyaren da ake yi a ofisoshin hukumar da wasu ƙananan hukumomi na daga cikin ƙoƙarin inganta wuraren aiki da kayan aikin gudanar da zaɓe.
Shugaban hukumar ya kuma buƙaci ma’aikata su gudanar da ayyukansu bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki, dokar zaɓe da ƙa’idojin INEC, yana mai jaddada cewa hukumar za ta tabbatar da gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci, gaskiya, haɗin kai da sahihanci.
“Mu ba ’yan takara ba ne, amma za mu yi duk abin da ya dace domin gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci, haɗin kai da sahihanci a shekarar 2027,” in ji shi.
An ƙara shirin tattara katunan zaɓe da inganta na’urori
Farfesa Amupitan ya jaddada muhimmancin tattara katin zaɓe na dindindin (PVC), inda ya umarci jami’an hukumar su ƙara wayar da kan jama’a, musamman a ƙananan hukumomi, domin masu rajista su karɓi katunansu kafin zaɓe.
Ya bayyana cewa karɓar katin zaɓe haƙƙi ne na ɗan ƙasa, ba wata alfarma ba, don haka ya buƙaci ma’aikata su tabbatar da cewa babu wani mai rajista da aka hana shiga harkokin zaɓe saboda rashin isasshen bayani.
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta riga ta karɓi wasu kayayyakin zaɓe waɗanda ba na sirri ba, yayin da aka ba da odar ƙarin na’urorin tantance masu zaɓe ta hanyar tsarin Bimodal Voter Accreditation System (BVAS), waɗanda ake sa ran isowarsu cikin makon.
Ya ce hukumar tana aiki kan samar da wuraren adana na’urorin, tare da kammala tantance na’urorin BVAS da ake da su a faɗin ƙasar, bayan ƙalubalen da aka fuskanta a zaɓen 2023.
Ya ƙara da cewa fasahar zamani za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tantance masu zaɓe da kuma isar da sakamakon zaɓe, yayin da hukumar ke ƙoƙarin ƙarfafa tsarin gudanar da ayyukanta.
Shugaban INEC ya kuma buƙaci ma’aikata su ware lokacinsu domin tallafa wa Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi, sakatarorin gudanarwa, shugabannin sassa da jami’an zaɓe na ƙananan hukumomi, domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin sauƙi da nasara.
INEC ta nemi goyon bayan Sarkin Gombe

A wani ɓangare na ziyarar, Farfesa Joash Amupitan tare da tawagarsa sun kai ziyarar ban girma ga Sarkin Gombe, Mai Martaba Dr. Abubakar Shehu Abubakar III, CFR, a fadarsa domin neman addu’a, haɗin kai da goyon bayan masarautar wajen shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Amupitan ya bayyana cewa tattaunawa da sarakunan gargajiya na daga cikin muhimman matakan da hukumar ke ɗauka domin ƙarfafa zaman lafiya, wayar da kan jama’a da kuma gina amincewa da tsarin zaɓe.
Ya buƙaci Sarkin Gombe da ya taimaka wajen wayar da kan al’umma su karɓi katunan zaɓensu, masu cancanta su fito su kaɗa ƙuri’a, sannan shugabannin siyasa su gudanar da kamfen cikin lumana da mutunta juna.
Ya kuma amince da cewa akwai ƙalubalen tsaro a wasu sassan ƙasar, yana mai cewa INEC na aiki tare da hukumomin tsaro, ciki har da ’yan sanda, Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro da shugabannin rundunonin tsaro, domin rage barazanar da za ta iya shafar masu zaɓe da kayayyakin gudanar da zaɓe.
A nasa jawabin, Sarkin Gombe, Mai Martaba Dr. Abubakar Shehu Abubakar III, CFR, ya yi maraba da Shugaban INEC da tawagarsa, yana mai bayyana ziyarar a matsayin wadda ta zo a lokacin da ya dace, musamman ganin yadda shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara ƙamari.
Sarkin ya bayyana cewa gudanar da sahihin zaɓe na buƙatar tsari mai kyau, ƙwarewa, adalci, gaskiya da haɗin kan jama’a.
Ya tabbatar wa hukumar cewa masarautar Gombe da sauran masarautun yankin Arewa maso Gabas a shirye suke su ba da goyon baya ba tare da nuna goyon bayan wata jam’iyyar siyasa ba, domin tabbatar da zaman lafiya da sahihancin zaɓe.
Ya kuma yi alƙawarin tallafa wa ƙoƙarin hana tashin hankalin zaɓe, kalaman tunzura jama’a da yaɗa bayanan ƙarya, tare da ƙarfafa gwiwar ’yan ƙasa su shiga harkokin dimokuraɗiyya cikin lumana.
Tun da farko, Kwamishinan Zaɓe na Jihar Gombe, Mukhtar Gajiram Umar, ya yi maraba da Shugaban INEC da tawagarsa, yana mai cewa ziyarar za ta taimaka wajen duba shirye-shiryen da ake yi da kuma inganta ayyukan hukumar a jihar.
A ƙarshen ziyarar, Shugaban INEC da tawagarsa sun ziyarci ofishin hukumar da ke Ƙaramar Hukumar Gombe domin tantance matakin shirye-shiryensa, sannan suka duba ma’ajiyar kayan aiki ta shiyya domin tantance yanayin kayayyakin da kuma tsarin jigilar kayan gudanar da zaɓe.
Hukumar ta ce irin waɗannan ziyarce-ziyarcen na daga cikin ƙoƙarinta na tabbatar da cewa dukkan sassan ƙasar sun kasance cikin shiri domin gudanar da babban zaɓen 2027 cikin lumana, gaskiya da sahihanci.


