Rundunar ’Yan Sandan jihar Katsina a Najeriya ta tabbatar da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa, Adamu Abubakar, sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai musu.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe 7:30 na dare, a gaban gidan malamin da ke Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma ta Jihar Katsina, inda wasu mutum biyu dauke da makamai, waɗanda suke kan babur, suka buɗe musu wuta, har suka yi musu raunukan da suka yi sanadin mutuwarsu.
Bayan samun rahoton faruwar lamarin, Jami’in ’Yan Sandan da ke kula da sashen Dutsin-Ma (DPO) ya jagoranci tawagar jami’an rundunar zuwa wurin da lamarin ya faru.
Nan take aka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti mafi kusa domin ba su kulawar likitoci, amma abin takaici, likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da cewa sun rasu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage ya bayar da umarnin tura jami’an dabarun yaƙi da aikata laifuka da sauran jami’an tsaro zuwa yankin.
Rundunar ta ce an fara gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ake ƙara ƙaimi wajen gano waɗanda ake zargi da aikata kisan da suka tsere, domin cafke su da gurfanar da su a gaban shari’a.
Kwamishinan ’Yan Sandan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, abokansu da mabiyansu, da kuma al’ummar Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma baki ɗaya bisa wannan babban rashi.
Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai ta cafke waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da an yi musu hukunci bisa doka.
Rundunar ta ƙara da cewa za ta sanar da jama’a duk wani sabon bayani da aka samu dangane da lamarin a nan gaba.


