Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
Published: August 12, 2026 at 1:16 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: August 12, 2026

Darakta Janar na Hukumar Hadakar Ayyuka a jihar Gombe, Builder Mahmood Yusuf, ya fara rabon kayan tallafi ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe.

Da yake magana yayin rabon kayan, Builder Mahmood Yusuf (Tauraron Akko) ya bayyana shirin a matsayin wani bangare na ribar dimokuraɗiyya da gwamnatin Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ke samarwa al’umma.

Ya ce shirin tallafin ya kuma kasance wata hanya ta nuna goyon bayansa ga Gwamna Inuwa Yahaya da sauran ’yan takarar da jam’iyyar (APC) ta tsayar, tare da jaddada kudirin jam’iyyar na inganta walwala da tattalin arzikin al’umma.

Shi ma da yake jawabi, Mana Jan Yankin na Hukumar Upper Benue Dadinkowa a jihar Gombe, Sarkin Shanun Yamaltu Alhaji Dr. Abubakar Muhammad Bello ya yaba wa Builder Mahmood Yusuf bisa wannan shiri, yana mai bayyana tallafin a matsayin matakin da ya zo a kan lokaci kuma zai yi matukar tasiri ga rayuwar wadanda suka amfana.

Ya ce wannan karamcin ba wai kawai zai taimaka wajen inganta rayuwar masu cin gajiyarsa ba ne, har ma zai taimaka wajen karfafa goyon bayan jam’iyyar APC daga matakin al’umma zuwa matakin jiha.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun bayyana godiyarsu ga Builder Mahmood Yusuf, inda suka ce kayan da suka samu za su taimaka musu wajen bunkasa sana’o’insu, karfafa hanyoyin samun abin dogaro da kuma samun ‘yancin kai ta fuskar tattalin arziki.

Taron ya samu halartar manyan baki da suka hada da Kakakin Majalisar Dokokin jihar Gombe, Abubakar Muhammad Luggerewo, Shugaban Ƙaramar Hukumar Akko, Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Barista Sani A. A. Haruna; da sauran shugabannin jam’iyyar APC, masu ruwa da tsaki da magoya bayan jam’iyyar daga Ƙaramar Hukumar Akko.

Kayayyakin da aka raba sun hada da babura, injinan nika, takin zamani da injinan dinki, wadanda aka samar domin tallafa wa mata da matasa su dogara da kansu, inganta rayuwarsu da bunkasa sana’o’insu.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sana'o'i, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
Next Post: 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Bankin Duniya Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Afirka Da Yankin Sahara Afrika
Anyi Janazar ‘Yan Shi’a 33 Da Aka Kashe A Masallacin Juma’a Sauran Duniya
Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai Afrika
Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Wajen Hakar Ma’adanai Dake Jihar Filato Najeriya
Ruwa Kamar Da Bakin Kwarya Ya Haifar Da Mutuwar Mutane A Nairobi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ukraine Ta Aika Tawagar Kwararru Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Gwamna Bala Kauran Bauchi Ya Koma Jam’iyar APM Afrika
  • Hukumomi A Kasar Syri Lanka Suna Kokarin Fidda Jirgin Yakin Iran Daga Kasar Afrika
  • Ruwan Sama Ya Dai-Daita ‘Yan Gudun Hijira A Gaza Labarai
  • Shugaban Rasha Yafara Ganawa Da Jakadun Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Ukraine Amurka
  • Jam’iyyar APC Ta Rantsar Da Sabbin Shugabanni a Jihar Neja Labarai
  • Kasashen Yankin Gulf Sun Bada Sanarwa Afrika
  • Nuhu Ribadu Ya Mika Dalibai 100 da Aka Ceto Ga Gwamnatin Jihar Neja Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.