Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta naɗa tsohon kocin Super Eagles, Augustine Eguavoen, a matsayin kocin rikon kwarya na ƙungiyar mata ta Najeriya, Super Falcons.
Eguavoen zai jagoranci Super Falcons a wasannin neman gurbin shiga Olympics na 2028, inda Najeriya za ta kara da Comoros a zagaye na biyu na gasar neman gurbin shiga gasar.
Super Falcons za ta kara da Comoros a wasanni biyu da za a buga a Remo Stars Stadium da ke Ikenne-Remo, a ranakun 9 da 13 ga Oktoba 2026.
Eguavoen zai samu taimakon Christopher Danjuma, kocin Nasarawa Amazons, da kuma tsohuwar ‘yar wasan Super Falcons, Yusuf, tare da Olatunji Baruwa, wanda a baya ya taba rike aikin horar da masu tsaron raga na Super Eagles.
Wannan shi ne karo na farko da Eguavoen zai jagoranci wata kungiyar mata a matsayin babban koci.
Naɗin nasa ya biyo bayan sallamar Justine Madugu da tawagarsa ta masu horarwa, bayan Super Falcons ta kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta mata ta 2027—karo na farko da Najeriya ta kasa samun gurbin gasar tun bayan fara gasar a shekarar 1991.
Yanzu Eguavoen na fuskantar babban ƙalubale na dawo da Super Falcons kan turbar nasara, musamman a gasar neman gurbin Olympics na 2028.


