Babban Kocin Zambia ta na fama da Rashin Lafiya, Mataimakinta Zai Karɓi Aiki
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Zambia (FAZ) ta bayyana rashin lafiyar kocin Copper Queens Nora Häuptle yayin da ƙungiyar ke ƙara himma wajen shirye-shiryen gasar cin kofin ƙasashen Afirka ta mata ta 2026 (WAFCON) a Morocco, in ji rahoton
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, FAZ ta sanar da cewa mataimakin kocin Charles Halubono zai ɗauki nauyin ƙungiyar a lokacin gasar cin kofin ƙasashe uku da ke gudana a Malawi.
Sakataren FAZ Machacha Shepande ya bayyana cewa Häuptle ta yi rashin lafiya mai tsanani a Switzerland kuma bata sami damar zuwa Lilongwe kamar yadda aka tsara a baya ba.
“Ana sa ran mai horaswar Nora za ta hade da tawagar Copper Queens da ta bar Lusaka zuwa Lilongwe a makon da ta wuce, amma sai ta sanar da mu cewa tana jin rashin lafiya kuma ba za ta iya tafiya ba,” in ji Machacha ta hanyar FAZ Media.

Ya tabbatar da cewa Halubono zai jagoranci kungiyar a duk tsawon gasar yayin da Häuptle ke murmurewa.
” Hukumar Kwallon kafa ta Zambia FAZ na fatan mai horaswar Nora zata samu sauki cikin sauri yayin da Copper Queens ke ci gaba da shirye-shiryensu don tunkarar gasar cin kofin kwallon Kafa na Mata WAFCON, 2026 da za’ayi a ƙasar Morocco.


