Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Sojojin Amurka Sun Kashe Wasu Fararen Hula Ba Dalili
Published: December 5, 2025 at 7:27 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: December 5, 2025

Rundunar sojojin Amurka ta ce ta kai hari a kan wani karamin jirgin ruwan da ake zargin na safarar muggan kwayoyi ne a yankin ruwa na kasa da kasa a gabashin tekun Pacific jiya alhamis, ta kashe mutane hudu.

Rundunar sojojin ta Amurka, ta fada cikinwata sanarwar da ta bayar a dandalin sada zumunta na X cewa bayanan leken asiri sun tabbatar da cewa jirgin ruwan yana dauke da muggan kwayoyi, kuma an kai masa hari a kan hanyar da masu safarar muggan kwayoyi suka saba bi a gabashin tekun Pacific.

A halin da ake ciki, ‘yan majalisar dokokin Amurka sun samu ganin takardar dake kunshe da takaitaccen bayani da ya tsara matakan da gwamnatin Trump take dauka na kai hari kan jiragen ruwan da ake zargin suna dauke da kwayoyi a tekun Pacific.

‘Yan majalisar suna daukar wannan takarda a zaman mai muhimmanci ga binciken da suke yi na wani harin da sojojin Amurka suka kai kan wani jirgin a ranar 2 ga watan Satumba, inda suka kashe mutane 11, cikinsu har da wasu mutane biyu da suka kubuta da rai daga harin farko da aka kai kan jirgin.

Wannan takardar da ta takaita bayanin tana dauke da shafuka biyu, kuma ta zayyana jerin masu bayarda umurni, da yadda gwamnatin Trump take amfani da bnayanan leken asiri wajen gano irin wadannan jirage.

‘Yan majalisar sun bukaci da a kawo musu cikakkiyar takardar wadda ke dauke da bayanin komai da komai game da hare-haren, amma ba a san ko ma’aikatar tsaro zata yarda su gani ba.

A halin da ake ciki dai, manyan ‘yan jam’iyyar Democrat a majalisar dokoki dake cikin wadanda aka yi ma bayanin wasu hare-haren da aka kai a tekun Caribbean sun fada jiya alhamis cewa hankulansu sun tashi da bidiyon da suka gani na wasu mutane biyu da suka kubuta da rai, amma sai aka kara kai musu hari aka kashe su, Sai dai kuma takwarorinsu na Republican sun kare wannan hari na biyu da cewa bai saba ma doka ba.

Babban dan jam’iyyar Democrat a kwamitin kula da ayyukan leken asiri a majalisar wakilai, Jim Himes yace sun ga mutane biyu wadanda ba su da wata hanyar da zasu iya zuwa wani wuri, da jirginsu da aka gama lalatawa, amma sai aka kashe su.

Yace wannan abu na daya daga cikin abubuwa mafi tashin hankali da ya gani.

Shi ma babban dan Demicrat a kwamitin kula da ayyukan soja na majalisar dattijai, Jack Reed, yace hankalinsa ya tashi matuka da wannan bidiyo da ya gani kuma ya kamata a sake shi jama’a su gani.

Amma kuma shugaban kwamitin ayyukan leken asiri na majalisar dattijai dan jam’iyyar Republican, Tom Cotton, cewa yayi shi abinda ya gani mutanen biyu suna kokarin su juya jirginsu da ya kife ne, dauke da muggan kwayoyi zuwa Amurka domin su ci gaba da fafatawa.

Amurka

Post navigation

Previous Post: CAN: Da Alamu Daliban St. Mery Na Cikin Koshin Lafiya
Next Post: Trump: Zamu Kawo Zaman Lafiya A Fadin Duniya

Karin Labarai Masu Alaka

Farashin Mai Ya Ragu A Kasuwar Duniya Amurka
An Kama Tsohon Jakadan Birtaniya A Amurka Peter Mandelson Amurka
Rundunar Sojin Iran Tace Harin Amurka Ya Kashe Musu Sama Da Mutane Dari Afrika
Iran Zata Mayarwa Amurka Martanin Harin Kharg Afrika
Ministan Kudin Botswana Yace Akwai Hasashen Cewa Tattalin Arzikin Kasar Zai Ragu Amurka
Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yaki Da Akeyi Tsakanin Isra’ila Da Amurka Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Trump: Washington Zatayi Cinikayya Da Indiya Amurka
  • Matasa Sun Sayawa Ferfesa Pantami Fom Din Takarar Gwamnan Gombe Afrika
  • NUJ: Akwai Bukatar Inganta Albashin ‘Yan Jarida A Najeriya Najeriya
  • Jami’an Tsaro: Babu Abun Tashin Hankali Kan Shawagin Jiragen Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NDPHC Ta Yi Alkawarin Tallafa Wa Gombe Wajen Inganta Wutar Lantarki Afrika
  • Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Kara Aika Sunayen Jakadu Ga Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Yau Litinin Ake Cigaba Da Shari’ar Najib Zarak Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.