Hukumar kula da rayuwar dabbobi ta majalisar dinkin duniya da masu kare hakkin dabbobi na Afurka sun nuna damuwa ga yanda Jakuna ke matukar raguwa a duniya, saboda kashe su da a ke yi don samun nama da kuma amfani da fatar su wajen magani da ‘yan kasar Sin ke amfani da shi.
A gaba daya duniya alkaluma da aka yi amfani da wata na’ura, na nuni da cewar akwai kimanin Jakuna miliyan 40 a doron kasa.
Lamarin ya ta’azzara bayan ‘yan kasar Sin sun zuba jarin fataucin Jakuna a Najeriya don amfani da fatar Jakin.
Hakan ya haddasa tashin gauron zabi na jakuna da kuma barazanar karar da su har da rahoton shigo da naman bayan sayar da fatar Abuja a soyawa jama’a a matsayin naman yau da kullum.
Tsohon dan majalisar wakilan Najeriya mai sha’awar lamuran kare dabbobi daga cutarwa, Garba Datti Muhammad, ya ce nan da shekara 5 matukar ba a dau matakan da su ka dace ba, Jakuna za su kare a duniya.
Garba Datti wanda ya gabatar da babban jawabi a taron hukumar kula da dabbobi ta majalisar dinkin duniya da ta Afurka, ya ce wasu kan yanka jakuna don amfani da fatar ko cin naman maimakon amfani da jakunan ga lamuran sufuri a karkara.
Datti ya kara da cewa yanzu a duk duniya kimanin Jakuna miliyan 40 a ke da su kuma a na cigaba da hallaka su da cutar da su ba tare da kula da lafiyar su ko gudunmawar da su ke bayarwa ga tattalin arziki ba.
Game da barazanar sayarwa jama’a naman da a ka haramta yankawa na jakuna, wasu manyan makiyaya sun fara tunanin bude mayankar zamani a manyan biranen Najeriya.
Isa Tafida Mafindi tuni ya kafa irin wannn mayankar da ta lashe Naira miliyan dubu goma sha biyar.
Wani abun takaici shi ne yanda mutane ke barin jakuna su hau manyan hanyoyi da dare da kwatsam mai tuka mota sai ya yi kicibis da jaki a tsakiyar titi da kan haddasa mummunan hatsari.


