Tsohon shugaban Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya zargi tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da hannu a kama shi da jami’an rundunar ‘yansandan Najeriya tayi a ranar Juma’a.
An kama Magaji ne a ofishinsa da ke Kano ta hannun wasu jami’an ‘yan sanda inda suka shaida masa cewa suna aiki ne da umarnin Sufeto Janar na ‘Yansanda.
Da yake zantawa da Manema labarai jim kaɗan bayan sakin sa a ranar Asabar, tsohon shugaban PCACC ya ce matsalarsa ta samo asali ne daga wasu korafe korafe da Ganduje da tsohon Manajan Daraktan Hukumar KASCO ta Jihar Kano, Bala Inuwa, suka shigar.
A cewarsa, Ganduje ya zarge shi da “ batanci” da suka shafi takaddamar shari’a da ake yi kan mallakar hannun jarin Gwamnatin Jihar Kano a kamfanin Dala Inland Dry Port Limited.
“Kun sani, tun da na bar kujerar shugaban PCACC, na koma aikin lauya gaba ɗaya, kuma ni ne babban lauya a shari’ar Dala Inland Dry Port,” in ji shi.
Ya bayyana cewa bayan kama shi, kai tsaye aka wuce da shi Abuja cikin tsauraran matakan tsaro.
“An kama ni, an tsare ni tsakanin jami’an ‘yan sanda zuwa Abuja, jami’ai biyu dauke da bindigogi a gefena, sannan wasu uku a kujerar gaba, aka tashi da ni daga Kano zuwa Abuja.
“Muka yi tafiya cikin dare har muka isa wajen ƙarfe 3:00 na asuba,” in ji shi.
Muhyi Magaji ya ƙara da cewa duk da ya dage yana neman a nuna masa takardar kama shi, jami’an sun ƙi nuna masa, suna cewa a Abuja za a gabatar masa.
Ya bayyana cewa an bayar da belinsa, sai dai an umarce shi da ya koma Abuja ranar Laraba tare da mika fasfon sa na fita ƙasashen waje.


