Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnatin Bola Tinubu Ta Raba Taraktoci Dubu Biyu Domin Inganta Noma
Published: February 17, 2026 at 2:06 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wasu sabbin taraktocin noma guda 2,000 domin bunkasa aikin noma na zamani a fadin kasar tare da nufin noma sama da hekta miliyan 1.5 a duk shekara.

Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ne ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da shirin a ranar Litinin a Abuja, inda ya ce wannan mataki wani gagarumin sauyi ne a bangaren noma karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cewarsa, an kaddamar da shirin ne a karkashin shirin gwamnatin tarayya na Renewed Hope National Agricultural Mechanisation Programme, wanda zai samar da taraktoci masu karfin aiki tare da na’urorin noma sama da 9,000 domin inganta yawan amfanin gona.

Ya bayyana cewa za a fara da tura taraktoci 600 a mataki na farko, sannan a biyo da wasu 750 da kuma 650 a matakai na gaba har a kai ga cika adadin 2,000 a fadin kasar nan baki daya.

Ministan ya kara da cewa ba za a bai wa mutane taraktocin a matsayin mallaka kai tsaye ba, sai dai za a mika su ga masu samar da ayyukan injinan noma (Mechanisation Service Providers), inda kowace na’ura za ta iya noma kusan hekta 600 a shekara.

Ana sa ran shirin zai taimaka wa manoma sama da miliyan 1.2 a duk fadin Najeriya, tare da inganta samar da abinci da kuma bunkasa tattalin arzikin karkara.

Hakazalika, ya ce gwamnatin ta samar da asusun tallafin noma na Naira biliyan 50 ta hannun Bankin Masana’antu domin saukaka harkokin zuba jari a fannin noma, yayin da aka kuma tanadi Naira biliyan 250 domin tallafa wa kananan manoma miliyan daya a daminar shekarar 2026.

Bugu da kari, gwamnatin ta shirya samar da motocin gyaran taraktoci guda 36, da kuma gina cibiyoyin kula da injunan noma guda bakwai a sassan kasar nan, tare da shirin kafa babbar masana’antar hada taraktoci da za ta rika samar da tsakanin guda 2,000 zuwa 4,000 a duk shekara.

Gwamnatin ta bayyana cewa wannan shiri zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, rage wahalar aikin noma, da kuma kara yawan amfanin gona domin tabbatar da wadatar abinci a kasar nan.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: Jagoran Addinin Kirista A Kaduna Ya Rabawa Fiye Da Musulmai Dubu Kayan Abincin Azumi
Next Post: Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi

Karin Labarai Masu Alaka

Hadakar Gwamnatin Najeriya Da Amurka Ne Suka Kai Hari Sokoto Najeriya
Yawan wadanda suka mutu a mummunan harin yanbindiga a Jihar kwaran Najeriya yakai 170 Najeriya
Kasashen Duniya Sunyi Tir Da Hambarar Da Gwamnatin Venezuela Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
“Hotuna” An Sako Daliban Makarantar St. Mary’s Su 100 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugabar Kungiyar Cinikayya Ta Duniya Ta Bukaci Kasashe Su Gyara Harkokin Cinikayya Afrika
Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Matatar Man Dangote Ta Kara Yawan Mai Dake Zuwa Kasashen Afirka
  • Kungiyar Kiristoci Ta Karyata Kubutar Da Mambobin Su A Kaduna
  • Mutane 27 Sun Rasa Rayukan Su A Najeriya
  • Shugaban Amurka Yayi Barazanar Kulle Wani Dan Jarida
  • Iran Zata Kawo Karshen Yaki Da Isra’ila Da Amurka

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Bola Tinubu Ya Saka Hannu A Dokar Zabe Najeriya
  • Matatar Man Dangote Ta Kara Yawan Mai Dake Zuwa Kasashen Afirka Afrika
  • Amurka Zata Aika Jiragen Yaki Biyu Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Abu Mafi Daukar Hankali A Wasan Dambe Na Yau Wasanni
  • Menene Illar Yada Labaran Karya A Kafofin Sada Zumunta Na Zamani Labarai
  • Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.