Iran ta kama wani jirgin dakon dannyen Mai da tutar kasar Eswatini, jiya Lahdi, jirgin ruwan wanda yake dauke da Mai lita dubu 350 da aka yi sumogal, kamar yadda kamfanin dillancin labarai Tasnim mai kwarya kwaryar cin gashin kai ya bada labari.
Wani kwamandan dakarun juyin juya hali yace rundunr ta kama wani jirgi shake da mai da aka yi sumogal nasa, sun tasa keyar jirgin zuwa tashar jiragen ruwa dake gabar Bushehr, bayan wani umarni da kotu ta bayar, kuma za’a sauke Man. Kwamandan ya kara da cewa ma’akatan jirgin su 13 galibi ‘yan kasar India ne, mutum daya daga wata kasa makwabciya.
Iran wacce ta fi ko wace kasa arhan Mai saboda talllafin gwamnati, da kuma faduwar darajar kudin kasar, tana fama da yaki da ‘yan sumogal mai ta kan iyakokinta, da kuma ta ruwa da ake kaiwa kasashen larabawa dake yankin Gulf.
A wani gefe kuma hukumomi a Senegal, suna fadi tashin hana kwarar Mai, bayan da ruwa ya fara shiga wani jirgin dakon Mai, kusa da gabar tekun Dakar, kamar yadda hukumomin kasar suka fada jiya Lahadi.


