China ta kaddamar da wani rawan daji a ranar talata na tsawon sa’o’i 10 inda tayi amfani da makamai da albarusai sosai a kewayen Taiwan, kwana na biyu da take kaddamar da irin wannan matakin soja mafi girma a kewayen tsibirin, da zummar yi wa yankin zobe da nufin yanke ta daga duk wata gudumawa daga waje idan har rikici ya barke.

Rundunar mayakan kasar mai kula da shiyar gabas tace zata ci gaba da rawar dajin har karfe 6 na yamma agogon GMT, matakin da take dauka sun hada daga cikin ruwa, da ta sama, da wasu sassa biyar kewaye da tsibirin, wadda hakan yake gwada kudurin dakarun China na yaki da duk wani yunkurin ballewa, da karfafa burin hadewa ba tare da wani bata lokaci ba.


