A karon farko a tarihin Najeriya, Majalisar Dokokin Kasa ta amince wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yin aiki da kasafin kudin shekara 2024 da na 2025 har zuwa watan Maris na shekara 2026 mai zuwa.

Wakiliyar GTA Hausa Medina Dauda ta hada mana rahoto kan dalilan da ya sa Majalisar ta aiwatar da wannan aiki, Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun amince da gyara kudurin dokar kasafin kudin shekara 2024 da ta 2025 inda aka dunkule kashi 70 na kudaden manyan aiyukan wadannan shekaru har zuwa watan Maris na shekara 2026 inda ake fatan kammala dukkan aiyukan a cikin lokaci kana a fara aiki da kasafin kudin shekara 2026 daga watan Afrilu.
Yan Majalisar sun goyi bayan kudurin wanda aka karanta kuma aka zartar da shi ta hanyar karatu na farko da na biyu da na uku a zama daya kamar yadda Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa Sanata Solomon Adeola Olamilekan ya baiyana mana bayan sun kammala zaman a jiya talata.
Olamilekan ya ce ana bukatar karin lokaci don baiwa Gwamnatin Taraiyya damar Kammala wasu aiyuka da ake ci gaba da yi a karkashin Kasafin kudin shekara 2025.
Olamilekan ya ce an yi wannan tsawaitawan ne saboda Najeriya za ta cigaba da gudanar da kasafin kudi guda daya rak daga watan Afrilun badi don inganta amfani da kudaden da aka ware da kuma ba da damar kammala muhimman aiyukan samar da ababen more rayuwa.

A bangaren Majalisar Wakilai kuma Dan Majalisa Daga Jihar Jigawa Abubakar Hassan Fulata yayi bayanin dalilin da ya sa Majalisa ta dauki wannan mataki na tsawaita Kasafin Kudin shekra 2924 da na 2025 din cikin gaggawa Majalisa ta tafi hutun karshen shekara sai ranan 27 ga watan Janairu na shekara 2026 za su dawo bakin aiki.


