Yau Alhamis shugaban Rasha Vladimir Putin, yayi magana da shugaban kasar Venezuel Nicolas Maduro ta woyar tarho, inda ya baiwa Madurn tabbacin hadin kai da goyon bayan Moscow ga gwamnatin kasar, yayinda tak kara fuskantar matsin lamba daga ketare, kamar yadda fadar kremlin ta fada.
Maduro yana fuskkantar matsin lamba daga shugaban Amurka Donald Trump cewa ya sauka daga mulki, yayinda Aurka take kara jibge sojoji a yankin na Carrebean.
A cikin wata sanarwa data fitar, fadar Kremlin tace shugabannin biyu sun bayyan burinsu na ci gaba da aiki a sassn da kasashe biyu suka kulla yarjejeniya aiwatar da da suka shafi tattalin arziki, da makamashi.
A gefe dya kuma, Amurka tace zata ci gaba da kam karin jiragen ruwa masu dakon mai a gabar ruwan Venezuela, bayan da ta kama wani jirgin dakn mai a jiya laraba. Matakin da Venuezel ta kira fashi.


