Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio yace take-taken kasar Rwanda a yankin gabashin kasar Kwango ta Kinshasa sun keta yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattaba ma hannu karkashin jagorancin shugaba Donald Trump na Amurka a Washington.
A cikin wata sanarwar da ya buga a shafin zumunci na X ranar asabar, Rubio yace a bayyane yake cewa take-taken Rwanda a gabashin Kwango sun keta yarjejeniyar zaman lafiyar, kuma Amurka zata dauki matakan tabbatar da cewa an cika alkawuran da aka yi ma shugaban Amurka.
Ranar jumma’a a zauren MDD, Amurka ta zargi kasar Rwanda da laifin rura wutar yaki da tashin hankali a saboda hare-haren da ‘yan tawayen kungiyar M23 da take marawa baya suke ci gaba da kaiwa, wadanda kuma ke neman gurgunta yunkurin Amurka na wanzar da zaman lafiya a yankin.
A ranar 4 ga watan nan na Disamba ne shugabannin Kwango Kinshasa da na Rwanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da shugaba Donald Trump na Amurka a birnin Washington DC.


