Jami’an soji a kasashen Thailand da Cambodia sun fada a laraba cewa sun fara tattauunawa da Ƙasashen batun tsagaita wuta, bayan da suka koma fagen yaki mai tsanani da yanzu suke yi na tsawon kwanaki 16, mutane akalla 86 ne suka halaka.
Wannan zaman shawarwarin yana zuwa ne kwanaki biyu, bayan da ministocin harkokin wajen kasashe dake kudu maso gabas na Asiya suka yi wani zama na musaman a Kuala Lampur, da nufin sake farfado da yarjejeniyar zaman lafiya da shugaban kasar Malaysia wanda shine shugaban kungiyar hada kan Ƙasashen da ake kira ASEAN a takaice da shugaban Amurka Donald Trump suka shiga tsakani aka kulla cikin watan Yulin bana.
Kakakin ma’aikatar harokin wajen Ghailanda Rear Admiral Surasant Kongsiri, ya fada a laraba cewa kwamitin kula da harkokin kan iyaka zai zauna na tsawon kwanaki uku, wanda hakan zai iya sa a cimma tsagaita wuta.
Idan har shawarwarin suka tafi yadda ake so, har hakan ya kai ga cimma yarjejeniyar inji Kwangsiri, matakin zai bada damar ministocin harkoin tsaron kasashen biyu su gana ranar 27 ga watan Disemba.
Rahotani daga yankin sunce an fara shawarwarin da la’asiyyar Laraba agogon GMT.


