Gwamnatin Tarayya Ta Ayana Ranakun Hutun Kirsimeti, Boxing Day da Sabuwar Shekara
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Alhamis 25 ga Disamba da Juma’a 26 ga Disamba, 2025 a matsayin ranakun hutun Kirsimeti da Boxing Day a fadin ƙasar.
Haka kuma, gwamnati ta ayyana Alhamis 1 ga Janairu, 2026 a matsayin ranar hutun bikin Sabuwar Shekara, domin bai wa ‘yan ƙasa damar shagulgula da murnar shiga sabuwar shekara miladiya.
Wannan na cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dr. Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Litinin, a madadin Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.
Sanarwar na nufin bai wa al’ummar Najeriya damar gudanar da bukukuwa cikin walwala da kwanciyar hankali, tare da ƙarfafa zumunci da zaman lafiya a tsakanin al’umma.


