Wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya ce gwamnatin shugaba Donald Trump ba ta gamsu da janyewar da aka ce kungiyar ‘yan tawayen M23 mai samun goyon bayan kasar Rwanda ta yi daga wani muhimmin gari a yankin gabashin Kwango ta Kinshasa ba.
Jami’in na Amurka ya bayyana wannan ma kamfanin dillancin labaran reuters ne a daidai lokacin da mazauna garin na Uvira dake bakin iyaka da kasar Burundi suka ce an ba hammata iska ranar talata a kusa da garin.
Kungiyar M23 ta kwace garin Uvira a ranar 10 ga watam Disamba, kwanaki kadan a baya da shugaba Felix Tshisekedi na Kwango da shugaba Paul Kagame na Rwanda, suka ranttaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Washington tare da shugaba Donald Trump.
A bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio yace ta-taken Rwanda a gabashin Kwango sun keta yarjejeniyar zaman lafiyar, kungiyar M23 tayi alkawarin janyewa daga garin.
A yayin da akasarin mayakan M23 suka fice daga garin na Uvira, jami’in na Amurka yace har yanzu basu gamsu cewa kungiyar ta janye baki daya ba, yana mai cewa sunyi imani har yanzu mayakan kungiyar suna nan kewaye da garin.
Wasu mazauna garion na Uvira sun ce har yanzu akwai mayakan M23 a cikin garin wadanda suka cire kayan soja suka sanya na ‘yan sanda.
Haka kuma a yau da safe an ji kararrakin harbe-harbe daga duwatsun dake kallon wata unguwa mai suna Kalundu a garin.


