Rundunar Sojin Saman ta Najeriya (NAF) ta sanar da samun gagarumar nasara bayan aiwatar da hare-haren sama guda biyu a Tudun Turba da kuma sansanin Kachalla Dogo Sule da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Daraktan hulɗa da jama’a na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin ya bayyana cewa an kai hare-haren ne ranar Lahadi bisa sahihin bayanan sirri daga majiyoyi daban-daban.
Ejodame ya ce hare-haren an kai su ne kan muhimman mafakan ’yan fashin daji da ke da alaƙa da hare-haren da aka kai kwanan nan a yankin Arewa maso yamma, inda aka tura jiragen NAF domin raunana ƙarfin ’yan ta’addan tare da hana su samun wuraren ɓuya.
A cewarsa, harin farko a Tudun Turba wanda aka tabbatar mafakar ’yan fashi ce ya lalata wani gini mai rufin sinki da ke zama cibiyar ayyukan sansanin.
“Binciken bayan harin ya tabbatar da rusa wurin gaba ɗaya tare da hallaka ’yan fashi da dama.
“Harin na biyu ya kai ga sansanin Kachalla Dogo Sule wuri ne da aka fi sani wajen kera na’urorin fashewa (IED) da kuma gudanar da ayyuka, kuma yana da alaƙa da hare haren da aka kai a kan hanyar Dan Sadau Magami.
An kai hari kan gine-gine da dama, lamarin da ya haddasa gobara mai tsanani wadda ta lalata kayayyakin aiki tare da hallaka ’yan fashin daji da dama, ta yadda aka lalata ƙarfin ƙungiyar wajen kerawa da amfani da IED,” in ji shi.


