Gobarar Daji a Birnin Los Angeles na jihar California.
A ranar 7 ga watan Janairu ne fari da iska me karfi suka kara tunzura gobarar daji da ta kunno kai a garin Los Angeles dake jihar California, inda ta yi sanadiyyar rayukan mutane 29, ta kuma kone dubbannan gidaje kurmus a unguwannin Pacific Palisades da Altadena masu yawan jama’a.

A watan Oktoba aka kama, Jonathan Rinderknecht da ake zargi da kunna wutar da ta jawo barkewar gaggarumar gobarar dajin da ta tafka barna a unguwar Pacific Palisades. Mr. Rinderknecht, mazaunin unguwar a da ya musanta zargin.
Hatsarurrukan Jiragen Sama daya bayan daya.
Ranar 29 ga watan Janairu wani jirgi na American Airlines yayi taho mu gama da wani jirgin soja me saukar ungulu, yayin da yake isa filin jirgin sama na Ronald Reagan da ke Washington DC, inda dukkan su suka fada kogin Potomac.

Duk mutane 64, da ke jirgin da kuma sosjoji 3 dake cikin jirgin me saukar ungulu sun rasa rayukan su.
Wannan shi ne babban hatsari na jirgi na farko a kasar tun shekarar 2009.
Kwana biyu kacal bayan wannan kuma, wani jirgi me daukar marasa lafiya ya fadi a garin Philadelphia a jihar Pennsylvania. Jirgin da ke dauke da wata yarinya, da mahaifiyar ta, tare da wasu mutane 4, bai fi minti daya da tashi ba daga filin jirgin sama na arewa maso gabashin Philadelphia ya fadi. Dukkanin mutanen dake cikin jirgin, tare da wani mutum daya a kasa sun rasa rayukan su.
Sannan kuma ranar 17 ga Watan Fabrairu wani jirgin Delta ya bintsire a yayin da yake sauka a filin jirgin sama na Torornto a kasar Canada. Duka mutane 80 dake cikin jirgin sun tsira da rayukan su, 21 sunsamu raunuka, biyu daga cikin su sun samu raunuka me tsanani.
Mutuwar dan wasan Hollywood da matar sa.
Ranar 26 ga watan Fabrairu ne aka tsinci gawar dan wasan kwaikwayo ene Hackman da matar sa Besty Arakwa a gidan su garin Santa Fe a jihar New Mexico. A lokacin ba’a san takamaimai me ya kashe su ba, abin da ya ja hankalin daukacin jama’a.

Daga baya masu bincike suka sanar a watan Maris cewa Arakwa, me shekaru 65, ta rasu ne a sanadin cutar hantavirus, da ake samu daga fitsari ko miyan beraye, shi kuma Hackman me shekaru 95 wanda ke fama da ciwwon zuciya, da rikicewar kwakwalwa, and ganin ya rasu ne mako daya bayan rasuwar matar tasa.
Ambaliyar Ruwa a Texas.
Da sanyin safiyar 4 ga watan Yuli, wanda shine ranar samun ‘yanci Amurka, ruwan sama me karfi ya jawo ambaliyar ruwa a jihar Texas.

Fiye da mutane 130 suka rasa rayukan su, cikin su a kalla 117 daga gundumar Kerr a cewar Jami’a. Da yawan gawawwakin an samo su ne a wani sansani, da ake Kira Camp Mystic, na yara mata ‘yan addinin Kirista.
Bryan Kohberger ya amsa laifin sa.
Matashi Bryan Kohberger da ake tuhuma da laifin kashe wasu dalibai 4 ‘yan jami’ar Idaho ya amsa laifin sa a watan makonni kafin a shiga kotu kan shari’ar kisan da aka yi a shekarar 2022.
Kotu ta yankewa Kohberger daurin rai da rai a gidan kaso.

Shari’ar Sean Combs.
Bayan shafe makonni takwas da aka yi ana shari’ar da ta dauki hankalin ‘yan kasa a wata babbar kotu a birnin Manhattan dake jihar New York a watan Yuli. Kotu ta kama babban mawaki Sean “Diddy” Combs da aikata lefuka biyu safarar mutane don aikata karuwanci, amma ta wanke shi kan manyan laifuka na badala da aikata barna.

Mawakin yanzu yana zaman gidan kaso na shekara hudu a wani babban kurkukun kasa da ke jihar New Jersey. Ya daukaka kara a kan tuhuma da hukuncin da aka yanke masa.
Kashe Charlie Kirk.
An kashe dan rajin ra’ayin mazan Jiya Charlie Kirk, a yayin da yake tsaka da gabatar da wani taro a jami’ar Utah Valley a garin Orem da ke jihar Utah.

Charlie Kirk me shekaru 31 a duniya ya kafa kungiyar matasa masu ra’ayin mazan jiya a, kuma taron da ya gabatar a jami’ar Utah Valley, shine taro na farko da a cikin tarurruka da yake son yi, inda ya gayyaci daliban jami’a domin su tattauna kan muhimman batutuwa.
Wanda ake zargi da kisan, Tyler Robinson me shekaru 22, ya tsere wajen, abin da ya sa aka bazama nemoshi. Robinson ya kai kan sa ga hukumomi a Daren 11 ga watan Satumba.
Lokacin da ake binne mamacin, matar sa Erika Kirk ta ce ta yafewa wanda ya kashe shi ta ce ba’a ramuwar gayya da gayya.

Mutuwar Rob Reiner da matar sa.
Ranar 14 ga Watan Disamba aka tsinci gawar wani babban darakta na Hollywood Rob Reiner da matar sa Michele Singer Reiner, da aka daddaba musu wuka a gidan su da ke birnin Los Angeles.
Sa’o’i bayan nan aka kama dan su Nick Reiner me shekaru 32, ana tuhumar sa da aikata kisan.


