A wasu al’amura daban-daban da suka faru cikin ‘yan makonni kalilan a yankin arewa maso gabashin Amurka da ake kira New England, barayi sun yi awon gaba da naman kaguwa da dodon kodi guda dubu 40, wadanda aka kiyasta kudinsu ya kai dala dubu 400, kimanin Naira miliyan 581.
Lamarin farko ya faru a garin Falmouth na jihar Maine, inda hukumomi suka ce wani ko wasu sun sace keji 14 cike da dodon kodi daga wata gonar da ake Kiwon su.
Sauran biyun sun faru ne a wani gari mai suna Taunton a Jihar Massachussetts, kimanin kilomita 255 daga inda aka yi na farko, a ranar 2 ga watan nan na Disamba. Sannan a ranar 12 ga watan Disamba, wani direban tirela na bogi yayi shigar burtu yaje aka masa lodin naman kaguwa da aka yi niyyar kaiwa kantunan Costco a jihohin Illinois da Minnessota.
‘Yan sanda suka ce dama an saba satar irin wadannan kayayyakin saboda kudin da ake samu da wajen saida su, amma kuma a ‘yan shekarun nan, abin ya kara yin muni.
Har yanzu babu wanda aka kama dangane da wadannan sace sacen.


