Kashe-kashen al’umma, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci dake aukuwa a Arewacin Najeriya sun kasance barazana ga zaman lafiya da ci gaba a yankin.
Rarrabuwar kawuna tsakanin al’ummomin yankin ta bangaren addini, kabila da siyasa, sun kara rincabewa da dai-dai tuwan samun hanyoyin dakile matsalolin tsaron.
Hajiya Aisha Aliyu dake aikin wanzadda zaman lafiya da taimaka wa wadanda suka shiga ibtila’i sanadiyyan rashin tsaro, tace ayyukan ta’addanci dake aukuwa a sassan kasar suna shafan kowa ne, ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.
Farfesa Chris Kwaja, malami a jami’ar Modibbo Adama dake jahar Adamawa yace rashin shugabanci na gari, na daga cikin dalilan da suka hana kawo karshen ta’addanci a Najeriya.


