Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

An Bukaci Mabiya Addinin Kirista Da Suyi Koyi Da Rayuwar Yesu
Published: December 25, 2025 at 2:24 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: December 25, 2025

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Taya Kiristoci Murna; Ya Buƙaci Su Ci Gaba Da Addu’o’in Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Jihar Gombe Da Najeriya.

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya taya al’ummar Kirista na jihar Gombe dama duniya baki ɗaya murnar bikin Kirsimeti na bana, inda ya bayyana bikin a matsayin lokacin dake karfafa ɗabi’un kauna, zaman lafiya, sadaukarwa da kuma haƙuri.

A saƙonsa na barka da Kirsimeti, Gwamnan yace bikin haihuwar Yesu Almasihu yana nuna muhimmin lokaci na yin nazari kan kyawawan halaye dake haɗa kan ƴan adam, ba tare da la’akari da addini ko asalinsu ba, sannan ya yi ƙira ga al’ummar jihar Gombe su ci gaba da ririta zaman lafiyan da suke yi da juna tare.

Gwamna Inuwa Yahaya yace jihar Gombe ta kasance misali mai kyau na jituwa tsakanin addinai daban-daban, inda mutane masu bambancin addini da ƙabilu ke zaune tare kuma suna aiki tare cikin girmamawa da fahimtar juna.

“Wannan lokacin biki yana tunatar da mu ikon ƙauna, tausayi da sadaukarwa waɗanda kyawawan halaye ne da ke da mahimmanci ga koyarwar Yesu Almasihu.”

“Waɗannan ɗabi’u suna da matuƙar muhimmanci wajen wanzar da zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna a jiharmu da kuma ƙasa baki ɗaya,” in ji Gwamnan.

Gwamna Inuwa Yahaya, wanda kuma shine Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa, ya yi ƙira ga Kiristoci su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwan wajen yin addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da wadata a faɗin jihar da Najeriya, musamman a wannan lokacin da ake buƙatar juriya da haɗin kai don shawo kan ƙalubalen tattalin arziki, tsaro da zamantakewa.

Ya kuma yi ƙira ga al’ummar jihar Gombe su ci gaba da jajircewa wajen tallafawa kokarin gwamnati na inganta walwalar jama’a.

Gwamnan ya tabbatarwa al’ummar Kiristan jajircewar gwamnatinsa na yancin yin addini, tabbatar da daidaito da kuma haɗa kan jama’a, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa zata ci gaba da damawa da duk al’ummar jihar a harkokin ci gaban da ake samu a jihar Gombe.

Ya kuma bayyana al’adar gwamnatin na bada tallafi ga kungiyoyin addini a lokutan bukukuwa don rage musu ɗawainiya, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin haɓaka haɗin kai da farin ciki tare.

Ya yi wa Kiristocin jihar Gombe da kewaye fatan alheri, farin ciki da cikar buri a bikin na Kirsimeti, yayin da ya yi ƙira ga duk ‘yan Najeriya su ƙara sadaukar da kansu ga haɗin kai, ‘yan’uwantaka da kuma zaman lafiya don ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.

Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC
Next Post: Fadar Shugaban Ƙasan Najeriya Ta Musanta Wani Labarin ƙarya

Karin Labarai Masu Alaka

Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika
Rashin Kyawun Hanyoyi Babbar Matsalace A Najeriya Afrika
Shugaba Tinubu Yasa Hannu Kan Dokar Kasafin 2026 Afrika
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Katsina Afrika
Ganduje Ne Yasa Aka Kama Ni Inji Muhuyi Magaji Najeriya
Gwamnatin Tarayya Ta Cire Sharadin Rubuta UTME Ga Masu Neman Shiga Kwalejojin Ilimi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kungiyar ISIS Ta Kashe Sojojin Amurka Biyu Amurka
  • Gwamnatin Jamhuriyar Nijar Na Kokarin Inganta Harkokin Noman Kasar Afrika
  • Yakin Iran Da Isra’ila Da Amurka Zai Shafi Kasashen Afirka – Masana Afrika
  • Gwamnatin Kasar Nijar Ta Kame Babban Dan Jarida Afrika
  • Kauran Bauchi: Muna Nan A PDP Daram! Siyasa
  • Sabuwar Dama Ga Masu Zaɓe: INEC Ta Tsawaita CVR Zuwa Ƙarshen Yuli Afrika
  • Rundunan  ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Ta Miƙa Miyagun Ƙwayoyi Da Ta Kama Wa NDLEA. Labarai
  • Gwamnatin Tinubu Zata Samar Da Wutan Solar A Jami’ar ADUST Wudil Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.