Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa Afrika
  • Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika
  • An Tsaurara Tsaro Yayin Da Tehran Ke Shirin Karɓar Masu Jimamin Ayatollah Khamenei Afrika

Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa
Published: July 1, 2026 at 7:00 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Hadejia ta Jihar Jigawa, wadanda suka da hada Cibiyar Fasaha ta Bola Ahmed Tinubu da Asibitin Wankin Ƙoda, Tituna da kuma Rumbum Tanada Abinci, domin bunƙasa ilimin fasahar zamani, ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya, inganta hanyoyi da kuma tabbatar da wadatar abinci, daidai da manufar Shugaban Ƙasa ta Renewed Hope Agenda.

Cibiyar Fasaha ta Bola Ahmed Tinubu, wadda Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) ta samar, za ta kasance cikakkiyar cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire da fasahar zamani.

Cibiyar ta ƙunshi dakin bincike na zamani (FabLab) don nazarin basirar AI, na’urorin mutum-mutumi (Robotics) da fasahar kiwon lafiya, tare da cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire mai amfani da AI da kuma habaka kamfanoni masu tasowa (Startup Incubation Centre). Har ila yau, an tanadi dakunan jarabawar kwamfuta (CBT), wuraren aiki na haɗin gwiwa, babban zauren taro na zamani da kuma masaukin ɗalibai mai ɗaukar mutane 60.

Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma ƙaddamar da Asibitin Sanata Oluremi Tinubu da Cibiyar Wankin Koda, wanda aka gina domin girmama ta, kuma gidauniyar FutureMap Foundation tare da eHealth Africa suka gina tare da cikakken kayan aikin likitanci na zamani, ciki har da na’urorin gwaje-gwaje da wankin koda, domin faɗaɗa samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummomin da ba su samun da isasshiyar kulawa.

Domin tabbatar da ci gaba da samar da ingantattun ayyukan lafiya, asibitin ya haɗa da dakunan gwaje-gwaje na zamani, cibiyar wankin koda, dakin tiyata da kuma sashen kula da mata masu juna biyu da haihuwa. Haka kuma, an tanadi tsarin samar da iskar shaka (oxygen) na zamani, yayin da cibiyar ke amfani da makamashi mai sabuntawa domin tabbatar da cewa babu katsewar ayyukan lafiya.

Da take jawabi yayin ƙaddamarwar, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta buƙaci matasa da su yi amfani da damar da cibiyar ke bayarwa domin ba da gudummawa wajen sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya ta hanyar fasahar zamani.

Ta kuma yabawa Darakta Janar na NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi, CCIE, bisa jajircewarsa wajen tabbatar da cewa al’ummomi a faɗin ƙasar nan suna cin moriyar fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire.

Ƙaddamarwar ta kasance wani ɓangare na ziyarar farko da Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kai Jihar Jigawa, inda ta kuma ƙaddamar da Shirin Rumbum Abinci na Ƙasa na Yankin Arewa maso Yamma, tare da buɗe wasu muhimman ayyukan more rayuwa, ciki har da Titin Bola Ahmed da Titin Oluremi Tinubu, wanda hakan ke ƙara nuna jajircewar gwamnatin Renewed Hope wajen faɗaɗa damar samun fasahar zamani, ingantaccen kiwon lafiya da ci gaban ƙasa mai haɗa kowa da kowa.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa
Next Post: Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa

Karin Labarai Masu Alaka

Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa Afrika
Gwamnatin Najeriya Ta Karyata Raɗe-Raɗin Canza Sunan Kasar Da Soke Shari’a A Arewa Afrika
Hukumar EFCC Ta Kama Dan Kasuwa A Kamaru Afrika
Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya Labarai
Wata Kotu A Abuja Ta Wanke Abba Kyari Afrika
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa
  • Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa
  • Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jam’iyyar ADC Ta Karbi Peter Obi Da Wasu Manyan ‘Yan-Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tawagar Shirya Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Ta Ziyarci Masarautun Jihar Labarai
  • Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Iran Da Amurka Sun Gindayawa Juna Ka’idojin Tsagaita Wuta Afrika
  • Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado Amurka
  • Shugaba Trump Yace Akwai Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Iran Afrika
  • Malami: Gwamnatin APC Ta Gaza – “Yan-Kasa Kuwa Na Da Katin Zabe” Labarai
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Ta Saka Takunkumi Visa Ga Wasu ‘Yan Rwanda Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.