A jihar Rivers ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar su 16 Sun Koma Jam’iyyar APC
Mambobin majalisar guda 16 sun sanar da ficewar su daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Kakakin majalisar dokokin jihar, Martins Amaewhule, ne ya bayyana sauya shekar a zaman majalisar da aka gudanar a yau Juma’a.
Amaewhule ya kuma tabbatar da cewa shi ma ya yi murabus daga PDP, tare da shiga APC kasancewar ya bi sauran ‘yan majalisar da suka sauya sheƙa.


