Dubban ‘yan kasar Somaliya sun yi zanga-zanga ranar talata a fadin kasar domin nuna rashin yarda da matakin da Isra’ila ta dauka na amincewa da ‘yancin yankin Somaliland, matakin da wasu kasashen fiye da 20 suka yi Allah wadarai da shi a zaman cin mutuncin diyaucin kasar Somaliya.
A halin da ake ciki, shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud ya sauka a Turkiyya jiya talata domin tattaunawa da shugaba Recep Tayyip Erdogan a bayan sanarwar da Isra’ila ta bayar.
A wajen wani zaman gaggawa na Kwamitin Sulhun MDD a ranar litinin Somaliya ta nuna adawarta da wannan mataki na Isra’ila tana mai cewa barazana ce ga tsaro a yankin.
Wakilin Amurka a majalisar ya jaddada cewa matsayin Amurka dai bai canja ba a game da Somaliya.
Somaliland, yanki mai mutane fiye da miliyan 3, ya ayyana ballewa daga kasar Somaliya a 1991 a lokacin da ake tsakiyar yakin basasa amma tun daga lokacin babu wata kasa da ta amince da ‘yancin yankin sai a makon jiya da Isra’ila ta yi.
A Mogadishu babban birnin Somaliya, dubban muta ne suka hallara a wajen gangamin da sanannun malaman addini na kasar suka gudanar suna masu yin tur da matakin na Isra’ila tare da yin kiran hadin kai wajen kare diyaucin yankunan kasar Somaliya.


