Ranar Litinin gwamnatin Uganda ta ce ta haramta yada rahotannin zanga-zanga, ko ‘ya mutsi da tada hankali kai tsaye a kafafen yada labarai, kafin gudanar da zabe, inda shugaba Yoweri Museveni ke neman zarcewa a mulkin da ya shafe shekaru 40 yana kai.
Hukumomi sun tare daruruwan masu goyon bayan ‘yan hamayya kafin zaben da za’a gudanar ranar 15 ga watan Janairu, wanda Museveni mai shekaru 81 zai kara karawa da mawaki me shekaru 43 da ya zame dan siyasa Bobi Wine.
Ma’aikatar bada bayanai, sadarwa, da fasaha ta ce an haramta yada zanga-zanga, fadace-fadace da taron mutane ba bisa ka’ida ba kai tsaye a kafafen talabijin, domin hakan zai iya jawo tashin hankali, ya sa mutane cikin firgici.


