Arteta: Muna buƙatar mu farkawa da kuma shiryawa a watan Janairu
Mai horas da ƙungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta ya bayyana cewa Arsenal za ta kasance a fadake kuma a shirye take ta yi sauye-sauye a lokacin Janairu dangane da abin da zai faru ba matsalolin raunin da suke fuskanta a yanzu.
Manyan ‘yan wasa kamar Martin Odegaard, Gabriel, William Saliba, Kai Havertz, Gabriel Jesus da Noni Madueke duk sun fuskanci matsaloli na rauni a wannan kakar wasa “in ji shi.
Arteta ya ce: “Dole ne mu kasance a shirye – da zarar mun sami dama na ingantawa da kare darajar ƙungiyar wajan samo wasu ‘yan wasan dangane da abin da zai faru, muna buƙatar mu kasance a shirye saboda hakan.
Saboda babu wanda ya san abin da zai faru tsakanin yanzu zuwa lokacin da za’a bude cinikayyan ai ƙwallon ƙafa ce.
Za mu kasance a faɗake kuma mu san inda haɗarin zai iya zuwa dangane da ƙungiyar kuma mu kasance a shirye idan har za mu yi wani abu.”
Mikel Arteta a taron manema labarai.
Mun gina ƙungiyar da zata ba mu damar lashe kofuna, saboda raunin da muke da shi. Don haka ƙungiyar muna buƙatar ‘yan wasa masu ƙoshin lafiya. Amma duk da haka ina farin ciki da yadda muke a yanzu duk da yanayin da muka shiga.

A yanzu haka dai Arsenal ta ci gaba da sa ido kan dan Wasan gaba Antoine Semenyo, mai shekaru 25, daga ƙungiyar kwallon kafar Bournemouth dan kasar Ghana.


