FIFA Ta Tabbatar Da Ranar 15 Ga Disamba Don Sakin Sunayen ‘Yan Wasa Kafin AFCON 2025
FIFA ta sanar da cewa mika sunayen ‘yan wasa na gasar cin kofin kasashen Afirka ta CAF (AFCON) ta Morocco 2025 zai fara a hukumance a ranar 15 ga Disamba 2025, bayan shawarwari masu amfani” da akayi da masu ruwa da tsaki da kuma hadin gwiwa da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF).
Shawarar da Ofishin Majalisar FIFA ta yanke, ta rage lokacin da kwana bakwai – wani mataki ya yi daidai da shirye-shiryen da aka yi na Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA Qatar 2022.
Gasar AFCON ta 2025 za ta fara daga 21 ga Disamba 2025 zuwa 18 ga Janairu 2026, wanda hakan ya sanya ta zama karon farko na gasar da aka shirya a lokacin Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
FIFA ta ce yarjejeniyar ta yiwu ne dalilin hadin kai da CAF ta nuna” don tabbatar da daidaiton mafita ga ƙungiyoyin ƙasa, da masu shirya gasa a lokacin kalandar ƙwallon ƙafa ta duniya mai cunkoso.
A wani ɓangare na shirin, FIFA ta kuma ƙarfafa ƙungiyoyin membobi da ke shiga gasar AFCON da kulub din da ‘yan wasansu za su iya samun kansu a gasar nahiyar a lokacin da za a fara tattaunawar ɓangarorin biyu.
Ana sa ran waɗannan tattaunawar za su taimaka wa ɓangarorin biyu su cimma yarjejeniyoyin aiki, waɗanda za su rage cikas.


