Gombe Ta Faɗaɗa Kasuwar Wutar Lantarki, Inda Ta Buɗe Kofofinta Ga Masu Zuba Jari a Fannin Samar Da Wuta Daga Hasken Rana, da Makamashi Mai Tsafta
Gwamnan jihar Gombe a Najeriya Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sake jaddada alƙawarin da gwamnatin jihar Gombe ta ɗauka na buɗe damarmakin kafa ƙananan tashoshin samar da wutar lantarki daga hasken rana, hanyoyin da za su samar da makamashi don noma, da samar da wutar lantarki ga masana’antu, da sauya shara zuwa makamashi da sauran fasahohin zamani a matsayin hanyar samar da arziƙi mai ɗorewa da ci gaba ga kowa a faɗin jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron tattaunawa kan Buɗe Sabbin damammakin Makamashi a Sashin Wutar Lantarki na Jihar Gombe, wanda Hukumar Sanar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara (REA) tare da haɗin gwiwar Gwamnatin jihar Gombe suka shirya, wanda aka gudanar a Otal din Transcorp Hilton dake Abuja.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana taron a matsayin kyakkyawan dandalin da ya dace kuma mai amfani, a yunƙurin da Gwamnatin jihar Gombe, da REA da sauran masu ruwa da tsaki ke yi na faɗaɗa hanyoyin samar da wutar lantarki mai inganci, mai rahusa da ɗorewa a matsayin hanyar zaburar da ci gaba.
Ya bayyana muhimman damammakin da jihar Gombe ke da su a fannin samar da makamashi mai tsafta, inda ya bayyana jihar a matsayin wacce ta fi zaman lafiya a Arewa Maso Gabas, tare da wadataccen hasken rana, da yalwatattun filayen da suka dace, da ƙaruwar buƙatar makamashi da kuma ɗimbin matasa masu kuzari.
A cewarsa, waɗannan abubuwan sun sanya Gombe a matsayi ta musamman don taka muhimmiyar rawa a sauyin makamashi a Najeriya, muddin aka tsara hanyoyin zuba jari, fasaha da haɗin gwiwa yadda ya kamata.
Gwamnan yace gwamnatinsa ta sanya makamashi a matsayin ginshiƙin kawo sauyi a fagen tattalin arzikin jihar.
Ya ambaci wassu ayyuka kamar samar da fitilun hanya masu amfani da hasken rana, da farfaɗo da cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko da makarantu masu amfani da hasken rana a dukkan ƙananan hukumomin jihar, da kuma gyare-gyaren da suka sanya Gombe ta zama wurin dake haba-haba da masu zuba jari.
Ya tuno cewa jihar ta zama ta farko a fagen sauƙaƙa kasuwanci a shekarun 2021 da 2022, wanda hakan ya nuna manufofinta da suka dace da masu zuba jari.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ƙara bayyana cewa Jihar Gombe ta yi amfani da cikakken damar da Dokar Samar da Wutar Lantarki ta 2023 ta samar ta hanyar kafa Dokar Wutar Lantarki ta Jihar Gombe ta 2025, wadda ya baiwa jihar damar samar da wutar lantarki, dako da rarraba ta, da kuma samar da kasuwar wutar lantarki ta ƙashin kanta.
Ya ƙara da cewa ana shirye-shiryen kafa Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Jihar Gombe don yin aiki tare da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) don ƙarfafa tsarin rarraba wutar, da sanya mitoci da kuma tsarin samar da cibiyoyin wuta masu cin gashin kansu.
Ya yabawa Hukumar Kula da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara saboda muhimmiyar rawar da take takawa wajen faɗaɗa damammakin samar da wutar lantarki ga al’ummomin da basu da ita da waɗanda bata wadace su ba, ta hanyar kakkafa ƙananan cibiyoyin wuta masu amfani da hasken rana, yana mai cewa irin waɗannan ayyukan suna da tasiri kai tsaye ga sana’o’i, da ƙananan kasuwanci, da ilimi da kuma samar da kiwon lafiya.
Ya tabbatar da cewa Jihar Gombe a shirye take ta zurfafa haɗin gwiwarta da hukumar don faɗaɗa samar da wuta da za ta yi tasiri ga jama’a.
Gwamnan ya jaddada cewa dole ne tattaunawar ta zarce batun zaƙulo damarmaki kawai, ya zuwa haɓaka damammakin da zasu samar da ayyukan da ƙarfafa ci gaban masana’antu da kuma samar da wutar lantarki mai ɗorewa ga al’ummomi.
Ya tabbatarwa masu zuba jarin cewa jihar a shirye take ta samar da filaye, tsaro, kyawawan manufofi da kuma amincewa cikin gaggawa don daƙile matsalolin zuba jari a makamashi mai tsafta.
Ya sanar cewa a watan Nuwamban da ya gabata, jihar ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna don aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawat ɗaya (1MW) a Talasse na Ƙaramar Hukumar Balanga, a ƙarƙashin yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu wanda ya ƙunshi gwamnatin jihar da ƙananan hukumomi ta hanyar haɗin gwiwa da hukumar bunƙasa ayyukan haɗin gwiwa, da kuma kamfanin Mids Dynamics Limited.
Yace Manajan Darakta da kuma manyan shugabannin hukumar ta REA ne suka shaida sanya hanu kan yarjejeniyar, tare da shirye-shiryen fara irin wannan aiki a Filiya na Ƙaramar Hukumar Shongom, da wasu wurare garuruwa 22 na faɗin jihar.

Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada burin jihar na dogon zango, kamar yadda yake ƙunshe a cikin Kundin Ci Gaban Jihar Gombe na Shekaru 10 (DEVAGOM 2021-2030), cewa shine tabbatar da ganin kowane gida, makarantu, asibitoci da sana’o’i suna da damar samun makamashi mai tsafta, mai ɗorewa da kuma rahusa don haɓaka aiki, da rage talauci da kuma gina tattalin arziƙi.
Ya yi ƙira ga cibiyoyin gwamnati, abokan hulɗan ci gaba, masu kuɗi, masu zuba jari, masu bincike da shugabannin al’umma su haɗa kai da jihar wajen amfani da damarmakin makamashi mai tsafta waɗanda suka dace da muhimman bukatun tattalin arziƙi.


