Gwamnatin Jihar Bauchi dake tarayyar Najeriya ta kaddamar da Kwamitin Cibiyar Koyon Harkokin Ma’adinai ta Alkaleri, Jihar Bauchi (MIABAS).
A yayin bikin kaddamarwar, Kwamishinan Harkokin Habaka Ma’adinai, Hon. Mohammed Maiwada Bello, ya yabawa hangen nesa da jagorancin Gwamnan Bala Mohammed, yana cewa cibiyar babban ginshiki ce da za ta inganta bincike, horaswa da kuma ƙwarewa a fannin ma’adinai.

Kwamishinan ya bayyana cewa MIABAS za ta taimaka wajen horar da matasa da kwararru a fannoni daban-daban kamar tono ma’adinai, sarrafawa, ƙara darajar ma’adinai da kuma kula da muhalli.
Hakan zai karfafa gina ƙwararru ‘yan gida, samar da ayyukan yi, da kuma tallafawa matasa a dukkan harkar ma’adinai.
An dora wa sabuwar kwamitin—wanda ya kunshi masana daga manyan ma’aikatu da cibiyoyi—alhakin kammala cikakken tsari na kafa MIABAS cikin watanni uku.

Kwamishinan ya bukaci mambobin su yi aiki da gaskiya da jajircewa domin gina cibiyar koyarwa da kirkire-kirkire ta ma’adinai wacce za ta amfanar da jihar nan da kasa baki ɗaya.


